Yan bindiga sun kashe Limamin Masallacin Juma'a da yaki yarda ayi a tafi da shi, sun sace yaransa


Tsagerun yan bindiga sun hallaka Babban Limamin Masallacin Juma'an Sabon Garin Bilbis dake jihar Katsina bayan kin yarda sun yo awon gaba da shi cikin gona. 

Limamin mai suna Malam Adam ya gamu da ajalinsa da safiyar Litinin a gonarsa dake wajen garin Faskari, rahoton Premium Times. Sabon Garin Bilbis, wani gari ne dake karamar hukumar Faskari ta jihar.Katsina, kuma mai iyaka da jihar Zamfara. 

Wasu yan ta'adda sun yi yunkurin awon gaba da Limamin gari guda amma yaki yarda su tafi da shi Limamin na aiki a gona tare da wasu yara mata dake taya shi aikin lokacin da yan bindiga suka far masa Sun hallaka dattijon kuma sun yi awon gaba da yara matan 

Tsagerun yan bindiga sun hallaka Babban Limamin Masallacin Juma'an Sabon Garin Bilbis dake jihar Katsina bayan kin yarda sun yo awon gaba da shi cikin gona. Limamin mai suna Malam Adam ya gamu da ajalinsa da safiyar Litinin a gonarsa dake wajen garin Faskari, rahoton Premium Times. Sabon Garin Bilbis, wani gari ne dake karamar hukumar Faskari ta jihar.Katsina, kuma mai iyaka da jihar Zamfara.

Wani mamban kwamitin Masallacin, Lawal Mamman, wanda ya sanar da mutuwar Limamin ya bayyana cewa yan bindigan sun kwashe yara mata dake aiki tare da Malamin lokacin da suka kai harin. 

A cewarsa, yan bindigan sun umurci Limamin ya bi su kan babur amma yace ba zai yi ba. 

A cewarsa: 

"Sun fara yi masa barazana da bindiga amma yace babu inda za shi duk da cewa sun ce zasu kashe shi." 

"Ya fada musu cewa yana da matsala a kafa kuma ba zai iya binsu cikin daji ba."

 "Bayan mujadalan, daya daga cikin yan bindigan yace kawai su kashe shi su bar waje. Haka kuma sun kashe shi suka tafi da matan." 

Source: Legit.ng 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN