Yadda 'yan bindiga suka kashe tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Zamfara - BBC News Hausa


Rahotanni sun ce 'yan bindiga dauke da makamai sun tare hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Lahadi, inda suka yi garkuwa da matafiya da dama.

Bayanai sun ce an samu asarar rayuka ciki har da wani tsohon dan takarar gwamnan jihar Zamfara Alhaji Sagir Hamidu.

Yan uwan marigayin sun tabbatar wa BBC Hausa faruwar al'amarin kuma sun ce ya gamu da ajalinsa ne lokacinda 'yan bindigar suka tare hanya.

Malam Mohammed Sirajo Hamidu kanin marigayin ne kuma ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun bude wuta ne lokacin da direban yayansa ya yi kokarin juyawa domin komawa Kaduna bayan da suka fahimci cewa sun fada tarkon masu garkuwa da mutane.

" Masu garkuwa da mutane ne suka tare hanya kuma suna zuwa sai suka tarar da abinda ke faruwa, ganin haka sai suka yi sauri suka juya, suna juyawa za su koma Kaduna sai wasu mutum uku suka fito daga cikin daji suka tsaya a gabansu su ka bude wa motarsa wuta,harsashi daya ya same shi a kirji, daya kuma a kafarsa".

Ya kuma ce 'yan bindigar sun yi awon gaba da jami'in dan sanda daya da ke tsaron lafiyar marigayin ya yin da dirbarsa ya kubuta

Kashi-kashi

Sai dai duk da cewa kawo yanzu ba a san adadin mutanen da 'yan bindigar suka yi garkuwa da su ba amma hotunan da wasu matafiya suka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna motoci da dama a kan hanya kuma ba bu kowa a cikinsu.

Wasu bayanai sun ce adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ya kai arba'in

Shafin PRNigeria ya ambato wani matafiyi da ya kubuta yana cewa 'yan bindigar sun tare hanya a kauyen Katari da misalin karfe biyu na rana inda suka shafe sama da sa'a guda suna barna.

Matafiyin ya ce " Sai da muka koma bayan da muka ji harbe-harben bindiga kuma mun tsaya a wani wuri mai tazara sosai da wurin da al'amarin ya faru.Bayan sa'oi biyu mun ga wasu motoci na bin dayan hanyar, daga nan mun ci gaba da tafiyarmu".

"An yi garkuwa da matafiya da dama ko sun tsere cikin daji saboda mung a motocci akalla 15 akan hanya kuma ba bu kowa a cikinsu lokacinda da muka wuce wurin da al'amarin ya faru", in ji shi

Sai dai har yanzu rundunar yan sanda jihar Kaduna ba ta ce komai kan al'amarin

Kauyen Katari na daya daga cikin wuraren da masu garkuwa da mutane ke tasiri a hanyar Kaduna zuwa Abuja . Ko a baya ma sai da yan bindigar su ka yi garkuwa da sarkin Bungudu na jihar Zamfarar mai martaba Hassan Atto.

Ya kubuta daga hannun 'yan bindigar bayan ya yi kwanaki 32 ana garkuwa da shi

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN