Yadda gazawar talaka ke zama ginshikin nassara ga makiyin talakawa


Kaso 70 na jami'an tsaron kasar Afrika ta kudu lokacin mulkin wariyar launin fata bakaken fata ne su kansu.

Kasar Britaniya watau Ingila, ta mallaki kasar Masar (Egypt) da karfin soji 80,000, amma 1000 kadai Yan asalin kasar Britaniya cikin adadin sojin, yayin da sauran sojin mutanen kasar India ne.

Kazalika kasar Faransa (France) ta yi nassarar mallakar kasar Syria da soji wadanda asali yan kasar Algeria ne da na kasar Senegal.

DARASI A NAN SHI NE

Gazawar al'umma ko talaka shi ne zai ba gurbataccen shugaba ko dan siyasa damar rusa rayuwar talaka.

Sanin ya kamata da fahimtar juna lokacin da ya kamata domin samun ci gaba cikin al'umma shi ne mafi dacewa da rayuwar talaka.

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN