An sami fashe-fashen wasu abubuwa guda biyu a tsakiyar babban birnin Uganda ranar Talata, wanda ya auku minti 30 daga tashin abin fashewa na farko, kamar yadda yansanda da wani dan Jarida da ke wajen da lamarin ya faru suka ambato ranar Talata. Shafin isyaku.com ya tattaro.
Fashewar farko ya auku ne kusa da ofishin Yan sanda na tsakiyar birnin, na biyun kuma ya tashi a kusa da ginin Majalisar kasar.
Babu wani bayyanannen dalili ko musabbabin wadannan fashe-fashen. Haka zalika babu kungiya ko wani da ya ambato daukar alhakin fashewar kawo yanzu.
Fashewar farko ya auku da karfe 10 na safe a Unguwar Buganda Road da ke birnin Kampala babban birnin kasar Uganda.
Reported by ISYAKU.COM
Domin samun labaran mu ta Whatsapp kai tsaye Latsa Link a kasa
https://chat.whatsapp.com/
Domin Tuntubar mu ko aiko Labari LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu LATSA NAN
Shafin mu na Facebook facebook.com/isyakulabari
Shafin mu na Twitter twitter.com/isyakulabari
Rubuta ra ayin ka