Babban magana: Gwamnatin Buhari za ta saka sabon haraji, 'Pure Water' zai koma N50 nan kusa

Kungiyar masu samar da ruwan sha ta Najeriya (WAPAN) ta bayyana cewa farashin ruwan ‘pure water’ na iya tashi daga N20 a yanzu zuwa N50 kan idan gwamnatin tarayya ta aiwatar da shirin haraji kan abubuwan shaye-shaye na yau da kullum. 

Shugaban WAPAN na kasa, Eneri Odiri Jackson ne ya bayyana hakan a wani taron da aka gudanar a Legas. 'Yan Najeriya sun shaidi tashin farashin ruwa sau uku a cikin shekarar 2021; daga N5 zuwa N10 da kuma N20. 

Kwamitin Majalisar Wakilai kan Kudi a watan Agusta 2021, ya yanke shawarar cewa za ta yi wa dokar Kudi kwaskwarima don dawo da haraji kan duk wani abin sha na yau da kullum. Shugaban WAPAN na kasa, Eneri Odiri Jackson, ya ce aiwatar da haraji kan sinadarai da ake amfani da su wajen samar da ruwa zai yi tasiri ga tattalin arzikin kasar, kamar yadda DailyTrust ta ruwaito. 

Jackson ya ce: “Babu shakka farashin pure water zai tashi daga N20 zuwa kusan N50. Ina ba da shawarar cewa gwamnati ta yi nazari hekara mai zuwa, kafin a ci gaba da aiwatar da manufar."

Kungiyar masu samar da pure water na ATWAP sun koka kan raguwar mambobi a kungiyar tasu. Mrs. Clementina Chinwe Ativie, shugabar ATWAP, ta ce mambobin kungiyar sun ragu da 16,000 sakamakon kalubalen tattalin arziki daban-daban, duk kuwa da cewa farashin pure water a kowace ya karu da fiye da 150% a cikin shekaru biyu da suka gabata. 

Legit Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Domin samun labaran mu ta Whatsapp kai tsaye Latsa Link a kasa

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin Tuntubar mu ko aiko Labari LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu LATSA NAN

Shafin mu na Facebook facebook.com/isyakulabari 

Shafin mu na Twitter twitter.com/isyakulabari 

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN