Wani dan sanda ya kashe abokinsa dansanda bayan zafafan cacan baki a wajen daurin aure (Hotuna)


Wani dansanda mai suna Sergeant Yerin Sapele ya mutu bayan an daba masa wuka a birnin Yenagoa na jihar Bayelsa. Shafin isyaku.com ya samo.

IgbereTV  ta ruwaito cewa abokin Yerin wanda shi ma dan sanda ne kuma abokinsa na kusa da shi ya kashe shi bayan zafafar cacan baki da ya kaure a tsakaninsu a wajen bikin daurin aure ranar Alhamis 4 ga watan Nuwamba 2021.

Sakamakon haka ya daba ma Yerin wuka kuma lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN