Tashin Hankali: Wata Budurwa ta mutu a dakin saurayinta daga zuwa ziyara


Kwalejin fasaha ta jihar Osun ta bukaci a gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar ɗaya daga cikin ɗalibanta mata mai suna Wumi. 

Jaridar Punch tace ɗalibar, wacce take shekarar karatunta ta ɗaya a sashin koyon aikin jarida, ta mutu ne ranar Asabar, bayan gajeriyar rashin lafiya a ɗakin Saurayinta.

 Rahotanmi sun bayyana cewa Wumi na fara nuna wasu alamu na rashin lafiya aka gaggauta kai ta asibiti mai zaman kansa a Iree, amma suka ƙi amsarta. 

Ɗalibar ta ƙarisa mutuwa ne yayin da ake kokarin canza mata wani Asibitin na daban. 

Shin ana zargin saurayin nata? 

Wata ɗaliba da suke karatun kwas ɗaya, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa jami'ai sun damƙe saurayin da zargin hannu a mutuwarta. Ɗalibar tace: 

"Wumi ta ziyarci gidan saurayinta a yankin Igaa dake Iree, ba zato sai ta fara fitar da kumfa daga bakinta. Nan take akai gaggawar kaita Asibiti a Iree, amma suka ƙi amsarta, kafin a kaita wani kuma ta mutu."

 "Ƙawayenta suka kai rahoto wurin yan sanda, nan take suka turo jami'ai, suka ɗauki gawarta zuwa ɗakin aje gawarwaki a Ikirun." 

"Saurayin na ta shima ɗalibi ne a kwalejin, jami'an yan sanda sun damke shi, sun tafi da shi ofishin su.

Kwalejin ta tabbatar da mutuwar Wumi Kakakin kwalejin, Tope Abiola, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya bayyana cewa wanda ake zargi ba ɗalibin su bane. 

Yace: "Eh, dagaske ne ɗalibar ND 1 dake karatu a sashin jarida ta rasa rasuwarta, amma ba mu san musabbabin mutuwarta ba." 

"Yan sanda na cigaba da bincike. Makaranta na yiwa iyayen ɗalibar ta'aziyyar mutuwarta, da zafi sosai matashiyar yarinya ta mutu ba zato ba tsammani." 

Source: Legit.ng 

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN