Tap di jan: Wani kyakkyawan saurayi ya auri mata 9 a rana daya saboda tsantsar soyayya - isyaku.com


Wani kyakkyawan matashi ɗan kasar Brazil, Arthur O Urso, ya shiga kundin tarihi na duniya bisa auren mata 9 a rana ɗaya saboda soyayya.

Rahotanni sun bayyana cewa Angon kyakkyawa ne sosai abin kwatance, kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito.

Meyasa Angon ya yi haka?

Mista Arthur ya bayyana cewa babban dalilinsa na yin haka shine don nuna tsantsar soyayya da kuma nuna adawa da auren mace ɗaya tilo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan aure na mata 9 da kuma angonsu kwara ɗaya ya gudana ne a wata cocin Katolika dake garin Sao Paulo na ƙasar Brazil a nahiyar Latin America.

Kafin wannan aure, shin angon yana da mata?

Tun kafin ɗaura wannan aure da ya kafa tarihi, Arthur yana da mata ɗaya mai suna, Luana Kazaki.

Lokacin da suka fita yawon cin amarci tsakanin Arthur da amaryarsa ta farko Luana, suka yanke shawara kan cewa ya kara auren mata 9 su cika goma.

Ma'auratan sun amince da wannan matakin ne domin nuna wa duniya cewa soyayya ba ta mutum ɗaya bace, ta kowa ce.

Rahotannin da aka tattaro a kafafen sada zumunta, sun tabbatar da cewa Arthur da Luana, sanannu ne a ɓangaren kwarewa a soyayya.

Kazalika ma'auratan sun yi ƙaurin suna wajen yaɗa hotunan su na batsa yayin da sukehutun cin amarci a garin Cap D’Agde na ƙasar Faransa.

Wannan birni ya shahara

Wannan birni dake ƙasar Faranta a yankin turawa, ya kasance makura a bariki, kuma har yanzun ana ta cece-kuce a kansa.

A garin dai an haramta yawo da kaya, hakan yasa Art

hur da Luana suka ci amarcin su a birnin kuma suna yawon buɗe ido babu tufafi a jikinsu.

Legit Hausa 

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN