Siyasar Najeriya: Jam'iyyar APC mai mulki ta dakatar da shugaban jam'iyya saboda abu daya


Jam'iyyar APC reshen jihar Ondo, ta dakatar shugabanta na Æ™aramar hukumar Ifedore, Mista Alex Oladimeji, bisa zarginsa da cin amanar jam'iyya. Punch ta bayyana cewa matakin dakatarwan na Æ™unshe ne a wata wasika mai É—auki da sa hannun mambobin kwamitin zartarwan APC a yankin. 

Shugabannin APC na yankin, sun bayyana Æ™arara cewa ayyukan da Oladimeji yake yi kwanan nan sun yi hannun riga da kundin dokokin jam'iyya. 

Meyasa suka dakatar da shugaban? 

Wani sashin takardar yace: 

Mu mambobin kwamitin zartarwa na ƙaramar hukumar Ifedore mun dakatar da Alex Akinyemi a yau 3 ga watan Nuwamba, 2021 daga jam'iyyar mu APC."

 "Mun É—auki wannan matakin ne sakamakon ayyukan cin amana da Anti-Party da yake yi wanda ya saba wa kundin dokokin jam'iyya." 

Wane irin rikici APC ta faÉ—a a Ondo? Shugaban jam'iyyar APC a jihar Ondo, Ade Adetimehin, ya bayyana cewa babu wani rikici da jam'iyyar APC ke fama da shi a kowane mataki na jihar. Ya kuma kara da jaddada cewa idan ma akwai wata matsala ta cikin gida a kowace Æ™aramar hukuma ce, to APC tana da hanyoyin warware ta. 

Yace: "A halin yanzu da nake magana daku, jam'iyyar APC a jihar Ondo na É—aya daga cikin reshen dake zaune lafiya a faÉ—in Najeriya." 

Muna da hanyoyin warware matsalolin mu na cikin gida a matakin jiha har zuwa gunduma, saboda haka rikicin Ifedore zai zama tarihi."

 Duk wani koÆ™ari na jin ta bakin shugaban da aka dakatar ya ci tura, domin wayar salulan shi bata shiga, kamar yadda TVC news ta ruwaito. 

Rikici dai yaÆ™i ci yaÆ™i cinyewa a majalisar tun bayan tsige kakakin majalisar, Ayuba Abok, tare da maye gurbinsa da Yakubu Sanda. 

A halin yanzun babu É—an majalisar da zai shiga zauren har sai mambobin sun warware matsalolin dake tsakanin su.

Legit Hausa
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN