Shin dagaske kasurgumin dan bindigan da ya addabi Arewa, Dogo Gide, ya mutu? Gaskiyar abinda ke faruwa



Rahotanni na ta yawo a kafefen watsa labarai cewa ƙasurgumin ɗan bindigan nan, Dogo Giɗe, ya mutu ta hannun mataimakinsa, Sani San Makama.

Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa mataimakinsa ya sheƙe shi ranar Lahadi da ta gabata.

Gide, ya gawurta a fagen satar mutane da dalibai, shine ya jagoranci kitsa sace ɗaliban FGC Yauri, a jihar Kebbi a watan Yunin da ya shuɗe.

Waye Dogo Gide?

Ainihin sunansa shine, Abubakar Abdullahi, kuma ɗan asalin ƙaramar hukumar Maru ne a jihar Zamafara, amma ainihin ƙauyen su babu wanda ya sani.

Ya fara ayyukan ta'addanci ne a dajin Kuyambana, inda yake kai hari ƙauyukan dake iyaƙar jihohin Kaduna, Kebbi da Neja.

Ya yi ƙaurin suna wajen garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, sayar dabbobi da kuma keta haddin mata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dogo Gide ya fito kowa ya sansa ne a shekarar 2018, lokacin da ya sheƙe mai gidansa, Buharin Daji. Kuma ya kashe wani jagoran yan bindiga, Damina, kwanan nan.

Wani masanin tarihi kuma mai bincike kan yan bindiga a Arewa maso yamma, Murtala Ahmed Rufa'i, yace Gide yana da karfin dukiya da kuma mutane da zai mallaki manyan makamai.


Rufa'i yace:

"Dukkan ƙungiyoyin yan bindiga (Gide da sauransu) suna da binidgu ƙirar AK-47 ko AƘ-49 sama da 500. Manyan ƙungiyoyin kamar na Gide, Mai Anguwa da Turji, suna manyan makamai kamar RPGGS da bindigar kaɓo jirgi."

Shin dagaske ne Dogo Gide ya mutu?

Duk da rahotanni da ake ta yaɗawa a kafafen watsa labarai, har yanzun babu tabbacin cewa Dogo Gide ya bakunci Lahira.

Majiyoyi da dama waɗan da ke da ilimi kan halin da yan bindiga ke ciki a Arewa ta yamma, sun sahida wa Premium Times cewa Gide yana nan a raye.

Ahmed Rufa'i ya maida martani kan wannan rahoton na mutuwar Gide da cewa, "Furofagandar sojoji ce kawai."

Wani tsohon ɗan jarida da ya yi aiki da HumAngle, Yusuf Anka, wanda ya jima yana rubutu kna yan bindiga a Arewa ta Yamma, ya musanta labarin.

Anka ya ƙara da cewa babu wani sahihin labari da ya tabbatar da mutuwar Gide, yace:

"Majiyar da nake da ita a yankin ya tabbatar mun cewa Gide yana nan da ransa. Labarin yana kafafen watsa labarai amma da na bincika sai na gano ba gaskiya bane."

"Giɗe yaje Ƙauyen Babbar Doka ranar Jumu'a, kuma ya shafe dogon lokaci a can, kafin ya fice da misalin ƙarfe 6:30 na yamma. Kuma ya koma ƙauyen ranar Lahaɗi da karfe 1:00 na rana, wannan shine kaɗai abinda na sani."

Wani ɗan fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, karkashin kungiyardu, Rundunar Adalci, Basharu Guyawa yace duk wata majiya da yake da ita ta ƙaryata labarin.

Yan bindiga
Bayan harin masallaci, yan Bijilanti sun kashe mutum 9, sun ƙona gidaje a wata rugar Fulani a jihar NejaHoto: dailytrust.com Source: UGC
Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa bayan harin ne, wasu yan banga suka hallaka dagacin garin Adogon-Mallam da ɗan uwansa.

Yadda lamarin harin ya faru
Ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya shafa, Shehu Mohammadu, yace:

"Yan bijilanti sun shigo ƙauyen mu, suka ƙona gidajen mu, sannan suka gudu. Matar ƙanina da ɗan jaririnta sun rasa ransu."
"Sun kuma kashe wani ƙani na, da ɗansa ɗan shekara 3, sun dai kashe mun yan uwana 7, kuma dole na gudu in ba haka ba nima su kashe ni."
"Mun bar ƙauyen, yanzun ina rayuwa a wani wuri mai nisa, kuma ba zan koma ƙauyen ba, domin nima kashe ni za su yi."
Wani shaidan da lamarin ya faru a idonsa, Alhaji Muhammadu Marike, yace yanzun haka yana gudun hijira ne a wajen jihar Neja.

"Banda harin da suka kashe dagacin garin Adogon Malam da ɗan uwansa, sun sake dawo wa. Sa'ar dana ci shine ɗaya daga cikinsu ya sanni, shine yace a kyale ni."
"Sun tafi da mutum 8, har yanzun babu wanda yasan inda suke. Mutanen mu sun tsere wuri mai nisa kamar Zaria da Kano."
Wane mataki yan sanda suka ɗauka?
Kakakin yan sanda reshen jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, yace hukumarsu ta tura da ƙarin jami'an yan sanda domin kame masu hannu a harin.

Ya kuma yi kira ga al'umma su taimaka wa jami'an tsaro da bayanan sirri domin tabbatar da doka ta yi aikinta akan waɗan da suka aikata wannan ɗanyen aiki.

Babbar jam'iyyar hamayya ta yi Allah wadai da harin, tare da kira a sako mutanen da aka kama cikin gaggawa domin su koma cikin iyalansu.

Legit Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN