Sheikh Giro ya baro gaskiya ya magantu kan wani halin Yan Najeriya, duba abin da ya ce


Shahararren malamin addinin islama, Sheikh Abubakar Giro Argungu, ya bayyana cewa kashi 85 cikin ɗari na yan Najeriya ba su da gaskiya wajen rike amana. 

Aminiya Hausa tace Sheikh Giro, ya yi wannan furucin ne a wurin wani taron wa'azi da aka shirya don murnar aure a jihar Nasarawa. 

Babban malamin ya yi kira ga yan Najeriya baki ɗaya su guji aikata cin hanci da rashawa, kuma su rinka kwatanta adalci da tsare gaskiya a rayuwarsu 

Addu'a ce kaɗai mafita a yanzu - Sheikh Argungu Shehin malamin ya bukaci mutanen Najeriya kada su gajiya, su cigaba da addu'a Allah ya kawo karshen ƙalubalen tsaro da yaƙi ci yaƙi cinye wa a ƙasar. 

A cewarsa a halin da kasar nan ke ciki yanzun, Addu'a ce kaɗai mafita ɗaya tilo da zata dawo da zaman lafiya da kuma dunƙulewa a Najeriya. 

Malamin yace: "Matuƙar muka dage da rokon Allah (SWA), to zai amsa mana ya kawo karshen ta'addancin yan bindiga, kuma ya kawo zaman lafiya da aminci, da kuma cigaban ƙasa." 

Malam Abubakar Giro, ya yi wannan kira ne a wurin taron wa'azin aure da ya gudana a Umaisha, karamar hukumar Toto, jihar Nasarawa. 

Legit.ng Hausa ta gano cewa an shirya wannan wa'azi ne domin murnar auren mata ta uku da kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Ibrahim Balarabe Abdullahi ya yi. 

Legit Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN