Najeriya zata iya gudanar da zaɓe ta Na'ura,Shugaban APGA ya magantu kan Anambra


Shugabam jam'iyyar APGA, Chief Victor Oye, yace yana da yakini Najeeiya zata iya gudanar da zabe ta na'ura kuma a tura sakamako ta na'ura. 

Channels tv tace Oye ya yi wannan furuci ne yayin da ake cigaba da karban sakamakon zaɓen gwamnan daga kananan hukumomin jihar Anambra ranar Lahadi. 

"Zamu iya kaɗa kuri'ar mu ta na'ura, wannan shine babban darasin da muka koya a wannan zaɓen, abu ne mai sauki gudanar da zaɓe da tura zaɓe ta na'ura."

Shin ya aka gudanar da zaɓe a Anambra?
Da yake magana kan zaben da aka gudanar ranar Asabar, Oyo ya bayyana cewa an yi komai cikin zaman lafiya, kuma za'a iya yin kwatankwacin haka a faɗin Najeriya.

"Babu wani zaɓe da zai fi wannan kwanciyar hankali, shine mafi kyaun zaɓe da muka taba yi a jihar nan. Zan iya cewa Najeriya zata iya tsaftataccen zabe fiye da haka."

Shin yan siyasa sun siya kuri'u?
A rahoton da suka fitar ranar Lahadi kan zaɓen, masu sanya ido sun bayyana cewa zaɓen ya gudana cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Meyasa suke son gwamnan ya nemi takara a 2023?

Da yake zantawa da manema labarai a madadin shugabannin jim kaɗan bayan taronsu, Saleh Mandung Zazzaga, yace gwamna Lalong zai ɗaga martabar ƙasar nan zuwa inda mutane basa tsammani.

A cewarsa sun yi wannan hasashen ne duba da nasarorin da ya samu na rikice-rikice da kuma yadda ya saita sabanin da ake samu na ƙabila ko addini a jihar Fitalo.

Ya ƙara da cewa duk da rikicin da ake samu nan da can, gwamnan bai yi ƙasa a guiwa ba wajen jawo kowane bangare a cikin gwamnatinsa.

Yace:

"Lalong ne yake jagorantar ƙungiyar gwamnonin Arewa, kuma mafi yawan mutaɓen wannan yanki na ma na waje na yaba wa da tsarin mulkinsa."
Lalong yana da kwarewar da Najeriya ke bukata.

Zazzaga ya kara da cewa gwamna Lalong yana da duk wata kwarewar siyasa wajen ɗaukaka Najeriya zuwa babban matsayi da kuma ƙara dankon haɗin kai.

Daga ƙarshe yace sun kammala shirin mara wa takarar gwmanan baya a 2023 kuma ba da jimawa ba zasu kaddamar da ita, amma a yanzun suna tattaunawar neman shawara ne daga kowane sashin ƙasar nan.

Gwamnan Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya sallami ciyamomi 21 da kuma kansiloli dake faɗin jiharsa.

A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ranar Alhamis, gwamnan ya gode wa ciyamomin bisa aikin da suka yi a jihar.

Source: Legit.ng

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN