Mun san ranar da za'a daina sata da garkuwa da mutane a Najeriya, Shugaban hukumar leken asiri


Shugaban hukumar leken asirin kudade watau NIFU, Mr Modibbo Tukur, ya bayyana cewa nan da watan Afrilun 2022, za'a daina sata da garkuwa da mutane a Najeriya. 

Hukumar NFIU wata sashe ce na Babban bankin Najeriy CBM dake bibiyan masu daukar nauyin yan ta'adda, da yaki da barayi masu kai kudaden Najeriya waje.

Moddibo ya bayyana hakan ne a taron waksho da aka shirya kan yaki da safarar kudade da kuma daukar nauyin ta'addancin ranar Talata a Abuja, rahoton DailyTrust. 

A cewarsa: "Ranar karshen yan bindiga da masu garkuwa da mutane tsakanin Maris da Afrilun 2022 ne." 

Yace ranar da 15 ga Satumba 2021 aka yi hasashe zai kasance karshe Boko Haram a Najeriya kuma an cimma wannan. 

A cewarsa, an cimma wannan nasara ne sakamakon toshe hanyoyin da yan ta'addan Boko Haram ke samun kudi kuma ya yanzu yankin Arewa maso gabas ta fi zaman lafiya da Arewa maso yamma dake fama da matsalar garkuwa da mutane. 

Source: Legit 

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN