Mene ne zaben Kato-bayan-kato, yaya ake yinsa, mene ne amfaninsa ko akasin haka?, Dalili da ya sa Gwamnoni ke adawar yinsa | ISYAKU.COM


Bayan an shafe shekaru ana taƙaddama kan yadda za a rinƙa gudanar da zaɓen fid da gwani a Najeriya, a kwanakin baya Majalisar Dokokin kasar ta amince da batun zaɓen fid da gwani ta hanyar ƴar tinƙe wanda aka fi
sani da ƙato bayan ƙato.

A halin yanzu shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ake jira ya saka wa kudirin hannu domin ya zama doka.

Da alamu wannan mataki na amincewa da wannan sabon tsarin ya yi wa ƴan ƙasar da dama daɗi ganin cewa za su samu damar shiga zaɓuka a duka matakai.

Sai dai jim kaɗan bayan wannan amincewar, ƙura ta fara tashi daga ɓangarori daban-daban musamman na 'yan siyasa inda wasu ke ganin bai kamata a tilasta wa jama'a gudanar da zabe ba ta hanyar ƴar tinƙe.

Ko a ƴan kwanakin nan sai da shugaban ƙungiyar gwamnoni na Jam'iyyar APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya yi fatali da zaɓe ta hanyar ƴar tinƙe, yana mai cewa yin hakan zai sa aiki "ya yi wa hukumar zaɓe ta INEC yawa."

A nata ɓangaren, jam'iyyar PDP ta bakin sakatarenta na ƙasa, Sanata Ibrahim Umar Tsauri, ta ce ba ta ga wani alheri tattare da tanadin da dokar zaɓen ta yi na tilasta wa jam`iyyun siyasa bin tsarin `yar tinƙe wajen gudanar da zaɓen fid da gwani ba, musamman ma a zaɓen `yan majalisun dokokin ba, face dora wa `yan majalisar ɗawainiyar da babu gaira ba sabar.

Mene ne zaɓen ƴar tinƙe?

Ganin cewa zaɓen ƴar tinƙe ba zaɓe ba ne da aka saba yi a Najeriya, wasu ba su taɓa ganin yadda ake yin sa ba.

BBC ta tuntuɓi Alhaji Shu'aibu Lili, wani tsohon ɗan jarida kuma mai sharhi kan siyasa da al'amuran yau da kullum.

A cewarsa, "yar tinƙe na nufin a sa layi kamar ƴaƴan carbi domin a zo a zaɓi ɗan takara". Kamar yadda aka saba a baya, akan yi amfani da mutane ƙalilan da ake kira wakilan jam'iyya ko kuma delegates a wajen zaɓe, amma a wurin ƴar tinƙe, duk ɗan jam'iyya zai iya layi domin ya yi zaɓe.

A cewar Alhaji Shu'aibu, "ba yau aka fara zaɓen ƴar tinƙe a Najeriya ba, domin lokacin gwamnatin Ibrahim Badamasi Babangida ma an yi.

A cewarsa, ƴar tinƙe na bayar da dama ga duk wani mai ƙuri'a damar zaɓen wanda yake so.

"Ƙuri'arka takobinka, idan kuwa za ka je ka yi yaƙi jazaman an ba ka damar da za ka je ka zaɓi ɗan takarar da kake buƙata, ba ɗan takarar da jam'iyya ta kawo maka ba ko kuma wanda yake jin cewa shi yake da wannan jam'iyya a aljihunsa ya kawo wani ya ce shi za a zaɓa.

Alhaji Shu'aibu Lili ya ce ɗaya daga cikin alfanun ƴar tinƙe ga dimokraɗiyya shi ne zai kawo ƙarshen amfanin da ake yi da maƙudan kuɗi.

"A duk lokacin da aka ce ga wani É—an takara ga kuma wani, za ka fahimci cewa akwai wanda jama'a suke so, akwai kuma wanda masu kwaÉ—ayi suke so ya ba su kuÉ—i, akwai kuma waÉ—anda suke sayar da kawunansu, don haka sai kana da kuÉ—i za ka É—auka," in ji shi.

"A irin wannan zaɓe, mutane sukan fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu su zaɓi wanda suke so a tsayar musu da takara. Idan aka tsayar da ɗan takarar wanda jama'a suke so, suka zaɓe shi, to sun riga sun gama yi wa ɗan takara aiki sun gama yi wa jam'iyya aiki, ya rage ga ɗan takara idan ya ci zaɓe ya yi aikin da ya dace."

Ya ce wannan tsari zai iya kawo ƙarshen siyasar uban gida domin a cewarsa, kowace siyasa yanzu a Najeriya akwai mai ita ko kuma akwai masu ita ko kuma waɗanda suke bayar da kuɗi a yi ta ko kuma waɗanda idan suka faɗa maganarsu ba ta tashi.

"Muna da mutane jajirtattu masu gaskiya waɗanda suka san mutuncin jama'a waɗanda za su iya fitowa su tsaya takara a kuma zaɓe su kuma shiga opis su kuma yi aiki," in ji shi.

Ya ce saboda abin da masu "Æ´an ba ni na iya" a jam'iyya ke yi na tsayar da mutane takara ke sa wa irin waÉ—annan mutanen kirkin ke jin tsoron fitowa takara saboda gudun cin mutunci.

Me ya sa gwamnoni suke adawa da zaɓen ƴar tinƙe

Wasu gwamnonin Najeriya sun fito ɓaro-baro sun nuna adawar su da wannan tsari na ƴar tinƙe da za a yi amfani da shi.

Alhaji Shu'aibu Lili ya shaida mana cewa ba yau gwamnoni suka fara tayar da haƙarƙari ba dangane da wani abin da za a yi domin gyaran ƙasa.

"Alal misali an yi hakan a kan cin gashin kai na majalisun jihohi da ƙananan hukumomi da kuma fannin shari'a duka babu wanda suka saka wa ƙuri'a suka ce suna so.

"Duk abin da ka gani cewa irin waɗannan mutanen ba su so, za ka ga cewa akwai wani abu da yake a ƙasa, in ji shi.

Haka ma BBC ta jiyo wani ɗan majalisar dattijai yana cewa ƴan majalisa sun yi wannan doka ne ganin cewa akasarin yan majalisar dattijan ƙarƙshin gwamnoni suke.

Ya ce za ka ga mutane sun fi son wani ɗan majalisa da gwamnansu wanda hakan zai iya sa wa idan gwamna zai ba da masu zaɓe wato delegate su yi zaɓe, tabbas tun zaɓen fid da gwani ɗan majalisar zai sha ƙasa, haka su ma ƴan majalisar wakilai suke fuskantar irin wannan matsala daga gwamnoni, in ji shi.

Ƙalubalen da za a iya fuskanta da zaɓen ƴar tinƙe

Kusan duk wani tsari da yake da amfani ba za a rasa ƙalubalen da ke tattare da shi ba.

Bisa wannan dalili, na tattauna da Malam Abubakar Kari, wanda malami ne a Jami'ar Abuja kuma mai sharhi ne kan harkokin siyasa.

A cewarsa, akwai ƙalubale uku da za a iya fuskanta a Najeriya dangane da wannan zaɓen na ƴar tinƙe.

Malam Kari ya bayyana cewa matsalar farko ita ce jam'iyya ce za ta gudanar da zaɓenta, kuma akwai ce-ce-ku-ce kan ko su wanene ƴan jam'iyya.

Ya bayar da misali da zaɓen fid da gwani da aka yi na Jam'iyyar APC a jihar Anambra inda ya ce ƴar tinƙe aka yi. "An ce Andy Uba ya samu ƙuri'u kusan dubu ɗari biyu da talatin kuma shi ya ci zaɓe, amma da aka zo zaɓe ɗubu arba'in da wani abu ya samu," in ji shi.

"Yawancin sunayen ƴan jam'iyyun na ƙarya ne, saboda haka shi wannan zaɓen na ƴar tinƙen zai iya kawo ce-ce-ku-ce."

Ƙalubale na biyu da Malam Kari yake ganin za a iya fuskanta shi ne batun bayar da kuɗi wurin zaɓe. Ya ce har yanzu masu hannu da shunu za su iya bin mutane har kan layi su ba su kuɗi amma ya ce a wannan karon ko za a bayar ba kamar da ba saboda akwai mutane da yawa tabbas kuɗin za su ƙaru.

Sai ƙalubale na uku da yake ganin za a fuskanta shi ne batun rikici ganin cewa mutane da yawa ne za su yi layi ga wannan layi ga wannan layi. Ya ce ana yawan samun hayaniya a wurin irin wannan zaɓen.

"Ana iya zuwa a taru a yi zaɓen, wasu ƴan daba su zo su fasa wurin", in j ishi.

Shi ma a nasa ɓangaren, Alhaji Shu'aibu Lili, ƙalubalen da za a iya fuskanta a yanzu wajen gudanar da wannan zaɓe shi ne rashin tsaron da ake fama da shi a wasu sassa na Najeriya.

Amma a cewarsa bisa abin da ya wakana kuma aka gan shi ba wai maganar hasashe ba, an yi zaɓen gwamna a jihar Anambra kuma an yi shi lami lafiya.

Za a iya cewa idan dai aka samar da tsaro a wuraren da za a yi wannan zaben ba za a samu cikas sosai ba.

Rahotun BBC Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Domin samun labaran mu ta Whatsapp kai tsaye Latsa Link a kasa

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin Tuntubar mu ko aiko Labari LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu LATSA NAN

Shafin mu na Facebook facebook.com/isyakulabari 

Shafin mu na Twitter twitter.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN