Matsalo ne, baya bani kuɗi: Matar aure ta haɗa baki da maza 3 don sace mijinta


Yan sanda a jihar Ogun sun kama wata matar aure Memunat Salaudeen kan zarginta da hada baki da wasu mutane uku don yin garkuwa da mijinta, rahoton Daily Trust.

Yan sanda masu sintiri a manyan hanyoyi ne suka kama wadanda ake zargin yayin da suke bincika motocci a kan hanyar Papa/Itori.

Kakakin yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya shaidawa manema labarai a ranar Talata cewa yan sandan sun kama maza uku - Olayinka Lawal, Asungba Nura da Usman Oluwatoyin kan babur kuma suka tsayar da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, yayin bincikarsu an gano adda da sabuwar igiya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Oyeyemi ya ce yan sandan sun raba su sannan suka musu tambayoyi kan abinda suke niyyar yi da addan da igiyan.

Mazan uku duk sun bada amsoshi daban-daban a cewar Oyeyemi hakan yasa aka zurfafa bincike.

Ya cigaba da cewa:

"Bayan tsananta tambayoyi, mazan uku sun amsa cewa wata mata mai suna Memunat Salaudeen ne ta basu N8000 su siyo adda da igiyar da za a iya daure dan adam da shi.
"Sun kara da cewa matar, wacce ma'aikaciyar jinya ce a unguwar Balogun tuntun Gas line Ifo, ta umurci su boye a wani hanya, za ta biyo da mijinta ta wurin sai su kama shi su daure sannan su bukaci kudin fansa."

Miji na matsalo ne, baya bani kudi, Memunat

Kakakin yan sandan ya ce matar auren wacce kuma ma'aikaciyar jinya ne ta amsa cewa ita ce ta kitsa yadda za a yi garkuwar.

Oyeyemi ya ce:

"Ta shaidawa yan sanda cewa mijinta baya bata kudi hakan yasa ta kitsa wannan garkuwar domin ta banbari kudi a hannunsa ko ta wane hali ne."

Kwamishinan yan sandan jihar CP Lanre Bankole ya bada umurnin a mayar da wadanda ake zargin sashin bincike masu garkuwa don zurfafa bincike.

Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

A wani rahoton, wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.

‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN