Matashi ya kulle mahaifiyarshi a daki ya banka wa gidan wuta saboda wani dalili, jama'a suna tsakar yi masa duka, duba abin da mahaifiyarsa ta yi


Wani matashi a unguwar Dagoreti da ke NairobiNairobi a kasar Kenya ya gurfana a gaban Kotu sakamakon banka wa gidan mahaifiyarsa wuta ya kone kurmus. An kiyasta darajar gidan a kan kudin kasar Kenya Ksh 1.3 miliyan dai dai da N4.7m  kudin Najeriya.

Shafin isyaku.com ya wallafa cewa Joseph Njuguna ya isa gida ne sai ya tarar cewa mahaifiyarsa bata gama abinci ba domin tana tsakar yin girki.

Ya tambayi mahaifiyarsa abincinsa, sai dai mahaifiyar ta ce ya jira domin sanwar na kan wuta. Sakamakon haka Njuguna ya fusata ya fita daga gidan.

Daga bisani ya dawo ya kulle mahaifiyarsa mahaifiyarsa da kwado a cikin gidan kuma ya banka wa gidan wuta. 

Mahaifiyarsa ta yi ihun neman ceto, daga bisani jama'a suka ceto ta. Sai dai gidan ya kone kurmus.

Njuguna ya gudu ya boye a gidan wani abokinsa, amma jama'a suka gano shi suka yi masa dukan fitar albarka albarka ala tilas mahaifiyarsa ta cece shi daga hannun fusatttun jama'a ta kai shi Asibiti aka yi masa magani.

Yan sanda sun gurfanar da shi a gaban Kotu sakamakon kone gidan mahaifiyarsa.

Reported by ISYAKU.COM

Domin samun labaran mu ta Whatsapp kai tsaye Latsa Link a kasa

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin Tuntubar mu ko aiko Labari LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu LATSA NAN

Shafin mu na Facebook facebook.com/isyakulabari 

Shafin mu na Twitter twitter.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN