Matar da ta fi kowa dadewa a doron Duniya ta mutu, duba shekarunta da kasarta (Hotuna)


Matar da aka yi Imani cewa ita ce mutum mafi dadewa a doron Duniya cikin wadanda aka taba samu wacce aka haifa a karni na 19 ta mutu. Shafin isyaku.com ya ruwaito.

Francisca Susano, wacce aka fi sani da  Lola Iska, ta mutu ranar Litinin da dare 22 ga watan Nuwamba a gidanta da ke kasar Philippines.

Tana da shekara 124 kafin mutuwarta. Wanda hakan ya sa ta zama mutum da ta fi kowa dadewa a doron Duniya.

Mahukunta a karamar hukumarta na haihuwa Kabankalan, da ke Negros Occidental, sun tabbatar da mutuwarta a shafinsu na sada zumunta.

City Government of Kabankalan ya ruwaito cewa: 

" Tare da nuna alhini da bakin ciki a zukatanmu, munsami Labarin mutuwar Lola Francisca Susano cikin daren ranar Litinin 22 ga watan Nuwamba*.


Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN