Malamin Addinin Musulunci Da CSP Na Bogi Na Cikin Waɗanda Suka Kutsa Gidan Odili


Da ake holen wadanda ake zargin a ranar Alhamis a sashin binciken manyan laifuka, CID, Garki Abuja, Kakakin yan sanda Frank Mba ya ce wadanda suka aikata laifin suna da sana'o'i daban-daban.

A hirar da ya yi da manema labarai yayin holen, DSP na bogi wato Ajojo ya bayyana cewa shi fa ba jami'in rundunar yan sandan Nigeria bane.

Mba ya ce cikin wadanda aka kama akwai dan jarida, da wani malamin addinin musulunci, sannan akwai wasu goma cikin wadanda ake zargin amma ba su shigo hannu ba.

Ya ce:

"Sufeta Janar na rundunar yan sandan Nigeria ya bada umurnin yin sahihin bincike a kan lamarin."

Tun da farko, Ministan shari'a kuma Antoni Janar ya rubuta wasika zuwa ga ofishin IGP yana neman a yi bincike kan lamarin domin gano wadanda ke da hannu da manufarsu.

Daga bisani aka tura binciken zuwa sashin binciken bayannan sirrri na yan sandan bisa umurnin IGP.

Yadda abin ya faru

A ranar 30 ga watan Oktoba ne wasu jami'an tsaro da suka hada da sojoji da yan sanda suka kutsa gidan alkalin kotun kolin kan zargin ana aikata abubuwan da suka saba wa doka a gidan.

Wani Lawrence Ajodo - da ya ce shi sufritandan yan sanda ne ya gabatar da takardan izinin binciken - amma yanzu an gano jami'in bogi ne.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa takardan izinin bincien da yan sandan suka gabatar a gidan Odili yana dauke da adireshin wani gida ne daban.

Abubakar Malami, Antoni Janar da Abdulrasheed Bawa, shugaban EFCC sun ce ba sune suka bada umurnin yin binciken ba.

Wata kotun Majistare da ke Abuja ita ma ta soke takardan izinin binciken da jami'an tsaron suka nuna a gidan kafin su shiga.

Daga nan ne sufeta janar na yan sandan Nigeria, Usman Baba ya bada umurnin a yi bincike.

Source: Legit

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN