Labari musamman: Yadda Yan bindiga suka farmaki Gidan-igwai a Sokoto suka kashe jami'in NSCDC (Hotuna)


Yan bindiga sun farmaki Unguwar Gidan-igwai da ke birnin Sokoto suka kashe jami'in rundunar NSCDC kuma suka bata motar aikin sintiri na rundunar. Shafin isyaku.com ya wallafa.

Wata majiya a Unguwar ta ce lamarin ya faru ne ranar Litinin 15 ga watan Nuwamba. Ya ce jami'in NSCDC ya rasa ransa ne lokacin da jami'an ke kokarin dakile harin Yan bindigan da ya auku da karfe 1:30 na dare.

Kazalika majiyar ta gaya wa Jaridar Premium times cewa "An kira yansanda lokacin da Yan bindigan suka shiga Unguwar, sai dai Yan sanda basu gan su ba saboda suna tafe da kafa ne ba a kan babura ba. Jami'an NSCDC sun fuskanci yan bindigan, sai dai Yan bindigan sun harbe direban motar jami'an sau uku, lamari da ya sa motar ta kauce wa hanya ta ci karo sakamakon haka wasu jami'an suka sami raunuka".

Shugaban karamar hukumar Sokoto ta arewa Mustapha Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya kuma yaba wa jami'an NSCDC bisa namijin kokari da suka nuna lokacin farmakin.

Ya ce jami'an tsaron hadin gwiwa na soji da yansanda sun taimaka wajen dakile hare-haren Yan bindiga Unguwar wanda ya yi fama da ire-ire wadannan hare-haren Yan bindigan a baya.Reported by ISYAKU.COM

Domin samun labaran mu ta Whatsapp kai tsaye Latsa Link a kasa

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin Tuntubar mu ko aiko Labari LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu LATSA NAN

Shafin mu na Facebook facebook.com/isyakulabari 

Shafin mu na Twitter twitter.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN