Labari mai zafi: An kama miyagun yan bindiga da Malamin duba a jihar Niger, duba abin da ya faru


Gwarazan yan sanda sun cafke wani ɗan shekara 50 a duniya, Umar Sama'ila, wanda ake zargin limamin duba na yan bindiga ne a wasu sassan Neja da Nasarawa.

Channels tv tace Kakakin rundunar yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, shine ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar a Minna, ranar Litinin.

Ya bayyana cewa an damke wanda ake zargin ne ranar Asabar bayan samun bayanan sirri cewa yan bindiga na shirin sace masu ibada a cocin Buku, yankin Abaji, Abuja.

Kakakin yan sandan yace:

"Yayin gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa ya kasance limamin duba na kasurguman yan bindiga da suka addabi Neja, Abuja da kuma Nasarawa."

"A tattaunawar da suka yi ta ƙarshe da tawagarsa a wannan ranar da aka cafke shi, ya umarce su, su kai hari cocin, kuma ya tabbatar musu zasu samu nasara."

"Ya kuma musu alƙawarin zai gudanar da addu'a domin a saki wani ɗan Bindiga 'Julli' dake tsare a hannun yan sandan Abuja."

Yan sanda sun cafke wasu 4

A cewar kakakin yan sandan, an damke Samaila ne kwana hudu kacal bayan jami'an yan sanda na caji ofis din Lapai sun samu nasarar kame wasu ɓarayin dabbobi.

Waɗan da jami'an suka kama sun haɗa da Abubakar Buba, Shehu Jare, Abubakar Garba, da kuma Abubakar Na'Allah, kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto.

Kazalika Aboidun ya bayyana cewa jami'an yan sanda da taimakon yan bijilanti sun samu nasarar kwato shanu 40 da tumaki 15.

"Yayin bincike mutanen sun amsa cewa suna kiwon shanu ne a wannan dajin amma sun gaza bayyana yawan dabbobin da suka mallaka."

Jirgin yakin rundunar sojin sama NAF na Operation Haɗin Kai sun aika dandazon mayakan ISWAP Lahira a Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa sojin sun gano tawagar masu karban haraji hannun mutane, inda suka sakar musu ruwan bama-bamai.

Source: Legit

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN