Kungiyar Bright Girls Organization ba kungiya ko jam'iyar adawa ba ce a jihar Kebbi - Abubakar ABK


Bayan dawowwar Kungiyar daga kasar India wurin Kai daliban su Karo na farko, sakataren  Kungiyar Abubakar Abk ya bayyana rashin jindadinsa akan watsa kasar da Kwamishannan ilimi Mai zurfi ya Yi masu a idanu a cikin Shirin "INA  MUKA DOSA"  tare da babban danjaridar nan na kasa wato Mungadi

"Wata daya kafin gudanar da jarabawar tantance daliban da mu ke son mu shigawa gaba su karanci likita, gwanna ya sani, bayan mun kammala ya sani domin har ya kira chairperson da Kansa ya jinjinawa kokarin da akayi. 

"Dr Zainab Shinkafi Bagudu ta kasance da Taron Kungiyar na gudanarda Hatsikan mata Dari a Na'ura, domin a taimaka masu su karanci sashen Lafiya. Sai dai abin mamaki, Kwamishannan Ilimi  Mai zurfi prof Muktar Bunza ya ki yabawa Kungiyar akan kokarin da tayi, ya Kuma Hana duk Wata dama da zata hada Kungiyar da Maigirma gwanna, ya cigaba da Yunkurin ganin kwannati ta Kai Yara sama ga Dari biyu batare da an jefa ko yaro Daya daka cikin Kungiyar ba. 

"Abin da ya bani mamaki;

1) Shin Yayan Wata jiha ce mu ka tantance?

2)Ko Kuma Yayan Wata jam'iya ce?

3) Ko Kuma yaran da iyayen su ba su da kuri'a ne?

4)Me yasa ake kokarin dole Sai an durkusa duk wani Abu da ba gwannati ta shirya ba?

5)Me ya janyo Kungiyar ta zama kishiya?

6)Shin ba damar Wata al'umma ta bayar da gudummuwa a jiha?

"A jawabin da muka sanarwa Duniya shine, Muna bayar da wannan gudummuwa domin yabawa da karfafawa Maigirma gwanna Amma ba mu Sami kuwalawa ko tallafi daga bangaren gwannati ba.

"Hakan bai Sanya mu ka Yi kasa a kuiwaba duk da cewa Duniya ta sani mu muka fara, muka Kuma Yi abinda al'umma su ka yaba, mun kwatanta adalci, mun Kuma Yi biyya iya gwargwado, Amma an watsa Muna kasa a idanu"

"Alhamdulillah! Mun Sami masu kishin kasa sun tallafa Kuma Kungiyar ta Sami nasarar Kai Kashi na farko a makarantar da tafi kowace makaranta ta kudi a India"

Muna godiya ga prof Tijjani Muhammad Bande, Maimartaba Alh Samai'ila Muhammad Mera CON, Maigirma Sanata Muhammad Adamu Aleiru, Alh. Kabiru Kamba, Alh Garba Nepa, Alh Yusuf Zero, Alh A I Suru, Dr Fatima Mustapha Bunza, Sherk Abubakar Giro Argungu, Engr Garba Ladan da Alh Abdullahi Bunza (Doja).

NB: Wannan rubutu, cikakken jawabin Sakataren kungiyar Bright Girls Organisation ne Abubakar ABK da ya rubuta da kansa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN