Kotu ta jefa Lauya Kurkuku kan zagin Kwamishana a Kano kan lamarin AndulJabbar


Kotun Majistare dake Gidan Murtala a jihar Kano ranar Talata ta jefa wani Lauya, Hashim Hussei Hashim gida gyara hali bisa zargin laifin zagin Kwamishana lamarin addinai, Tahir Adam.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa baya Lauyan ya saki bayanan rediyon inda ya caccaki Gwamnatin jihar Kano kan gurfanar da Malam Abduljabbar Kabara, kabara a kotu.

Lauyan yace sam Abduljabbar Kabara bai yi maganar batanci ga annabi ba.

Sakamakon haka, babban Limanin Masallacin Kwantin Kwari, Albakari Mika’il, ya kai Lauyan kara kotu kan yada labarin karya kansa da na kwamishanan.

A bidiyon jawabin, Lauyan ya ce Kwamishanan mugun mutum ne kuma shaidanin boye da kuma wasu kalaman batanci.

Amma yayin da ya gurfana a kotu, ya musanta haka kuma abokan aikinsa lauyoyi suka yi rokon a basa beli da sharadin ba zai sake irin wadannan kalamai ba.

Ya saba sharrudan beli
Amma bayan ba shi beli, lauyan ya sake sakin wani bidiyon inda yake alfahari babu wanda ya isa ya taba shi.

Shi yasa da aka koma kotu ranar Talata, Lauyan Kwamishanan, Lamido Sorondinki, ya bukaci kotu ta janye belin saboda Mr Hashim ya saba sharadin da aka sanya masa.

Alkali kotun, Hauwa Minjibir, tace a jefashi kurku zuwa karshen Nuwamba.

Lauyan yace:

"Da farko ya ce ayi hakuri. Yayi nadama cewa ba zai sake ba. Hakan na nufin cewa ya amsa laifinsa. Sai kotu ta jefashi gidan gyara hali cuwa 30 ga Nuwamba don cigaba da sauraran kara."

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN