Kotu ta daure lauya shekaru 15 bisa laifukan tafka karya a gaban kotu


Mai shari’a Mojisola Dada ta kotun hukunta manyan laifuka da ke zama a Ikeja a jihar Legas ta daure wani lauya Kenneth Ajoku hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari tare da zabin biyan tara bisa laifukan karya da kuma kirkirar shaidar karya. 

Alkalin kotun ya kama shi da laifuka biyu a cikin wasu tuhume-tuhume biyun da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta fifita a kansa, Tribute Nigeria ta ruwaito. 

Rahoto ya ce an fara tuhumar Ajoku ne tun a shekarar 2017 lokacin da hukumar EFCC ta samu bayanan sirri game da gungun ‘yan damfara da ke siyar da kadarorin gwamnatin tarayya 

Bayan bincike cikin tsanaki, EFCC ta ce an gayyaci Ajoku da tawagarsa zuwa hukumar, amma ya ki zuwa yayin da aka bukaci ganinsa a lokuta da daban-daban. 

Jami’an hukumar sun ziyarci ofishin wanda ake tuhuma, amma ba a same shi ba. A wani yunkuri na kawo cikas ga binciken, Mista Ajoku ya tunkari alkalin babbar kotun tarayya da ke Ikoyi, Legas, Ibrahim Buba, domin ya rantse da cewa jami’an hukumar sun kama shi tare da tsare shi a ranar 4 ga Mayu, 2017. 

Ya kuma bukaci a biya shi diyyar Naira miliyan 300. Kotun dai ta ki amincewa da bukatar ta kuma umarce shi da ya gabatar da kansa domin binciken hukumar EFCC. 

Daga nan sai ya garzaya zuwa kotun daukaka kara da ke Legas, a wani mataki na dakatar da binciken da hukumar EFCC ke yi masa. Kotun daukaka kara, itama ta yi watsi da daukaka karar. 

Daga nan aka gurfanar da shi a gaban kotu bisa tuhume-tuhume biyu da suka hada da karya da kirkirar shaidun karya, wanda aka ce ya sabawa sashe na 85(1) 86(1) da 88(1) na dokokin laifuka na jihar Legas, 2011. Ya musanta tuhumar da EFCC ta ke yi masa, sannan aka ci gaba da shari’ar gaba daya. 

A yayin shari’ar, lauyan masu shigar da kara, Franklin Ofoma, ya kira shaidu uku tare da gabatar da wasu takardu da kotun ta amince da su a gabanta. Da take yanke hukunci a ranar Juma’a, 29 ga watan Oktoba, 2021, Ms Dada ta kama shi da laifuka biyu, sannan ta yanke masa hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari, tare da zabin tarar Naira miliyan 2.5, kamar yadda Punch ta ruwaito. 

Legit Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN