Mabiyanmu su sani, akwai 'yan takara 18 ne suke fatan maye gurbin Gwamna Willie Obiano.
Daga cikinsu akwai:
Charles Soludo - APGA Senator
Andy Uba - APC
Valentine Ozigbo- PDP
Sanata Ifeanyi Ubah - YPP

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta bayyana, akwai akwatuna 1,820 da za su karba masu kada kuri'a 846,994 a mazabar Anambra ta arewa.
A mazabar Anambra ta tsakiya, za a samu akwatunan zabe 3,987 wadanda za su karba masu kada kuri'a 887,295 da suka yi rijista.
A Anambra ta kudu, za a samu akwatunan zabe 1,934 domin masu kada kuri'a 794,203.
Jimillar masu kada kuri'a da suka yi rijista sun kama 2.52 miliyan. Su ne za su fitar da makomar dan takarar da zai shugabanci jihar a shekaru hudu masu zuwa.
Legit.ng na nan daram a Anambra domin kawo muku bayanai kan yadda zaben ke tafiya. Ku kasance tare da mu!
Jami'an tsaro sun mamaye rumfunan zabe a Awka
Jami'an tsaro sun mamaye rumfunan zabe da ke Akwa, a jihar Anambra


Dan takaran jam'iyyar, Valentine ya dira rumfar zabensa don kada kuri'a
Dan takaran jam'iyyar, Valentine Ozigbo, tare da iyalinsa sun dira rumfar zabensa dake Social Centre, Amesi, karamar hukumar Aguata don kada kuri'arsu.

Gwamna Willie Obiano da matarsa sun kada kuri’a
Gwamna Willie Obiano da matarsa, Ebelechukwu sun kada kuri’arsu a rumfar zabe ta Eri Primary school, PU 004, Otuocha 1, Aguleri, karamar hukumar Anambra ta gabas da misalin karfe 9:28 na safe.
Gwamnan wanda ya zanta da manema labarai jin kadan bayan kada kuri’arsa ya ce:
“Na bukaci mutanen Anambra da su fito su yi zabe. Ko ina akwai zaman lafiya. Ku fito ku yi zabe.”

Masu kada kuri'a sun balle zanga-zanga kan dokar INEC ta hana marasa takunkumi zabe
Masu kada kuri'a a gunduma ta 9 da ke Ezimezi a Amawbia, karamar hukumar Awka ta kudu, sun balle zanga-zanga kan dokar INEC ta hana marasa takunkumin fuska saka kuri'a.
Masu zaben sun dinga tururuwar fitowa tun wurin karfe 8:30 amma sai aka ce su koma gida tare da sako takunkumin fuska, Punch ta wallafa.
Wannan lamarin ne yasa tsohon dan majalisar jihar Anambra, Chikodi Aghanya ya kwatanta lamarin da 'shirme'

Na'urar BVAS ta mazabar Soludo ba ta aiki
Masu kada kuri'a sun fusata. Kamar yadda suka ce, na'urar BVA ba ta aiki a mazabar dan takarar Charles Soludo.
"Babu abinda ke aiki a nan, ga katin zabe na," wani mai kada kuri'a ya sanar da Arise News TV.
Mazabar Sanata Andy Uba
Har yanzu jami'an INEC ba su iso mazabar Andy Uba ba, kamar yadda Arise TV ta wallafa
An fara kada kuri’a a zaben gwamnan Anambra na 2021
Da misalin karfe 8:30 na safe, an fara kada kuri’a a rumfar zaben PU005, Umudioka, karamar hukumar Dunukofia da rumfar zabe ta Area 13, Ichida 1, karamar hukumar Anaocha.
Rumfar zabe: Eri Primary school, PU 004
Rumfar zabe: Eri Primary school, PU 004, Otuocha 1, Aguleri, karamar hukumar Anambra ta gabas.
Har zuwa karfe 8:00 na safe, jami’an INEC suna nan suna shirye-shirye, sannan akwai masu jefa kuri’u yan kadan da ke duba sunayensu.
A wannan rumfa ne Gwamna Willie Obiano zai kada kuri’arsa.
Rumfar zabe: PU001 – Kindergarten Primary School, Obuofu 1
Rumfar zabe: PU001 – Kindergarten Primary School, Obuofu 1, Ward 05, Abagana III, karamar hukumar Njikoka.
A PU001, jami’an INEC na nan suna manna sunayen masu zabe da aka yi wa rijista, da kuma kafa rumfar zabe.
Zuwa yanzu masu jefa kuri’u uku sun hallara. Gaba daya an yi wa mutane 516 rijista, a bisa rahoton The Cable.
Dan takaran jam'iyyar AAC, Chidozie Nwankwo ya janye daga takarar zaben gwamnan Anambra
Dan takara jam'iyyar jam'iyyar African Action Congress AAC, Chidozie Nwankwo, ya janye daga takarar kujeran gwamnan jihar Anambra.
Nwankwo ya sanar da cewa dukkan wadanda sukayi niyyar zabensa yanzu kawai su goyi bayan dan takaran jam'iyyar PDP, Valentine Ozigbo.
Rahoto BBC

Ba za a yi zabe ba a rumfunan zabe 86, in ji INEC
Yayin da yan Anambra ke shirin zabe, a lura cewa hukumar INEC ta bayyana a baya cewa ba za a yi zabe ba a rumfuna 86 cikin rumfunar zabe 5,720 da ke jihar saboda basu da masu jefa kuri'u.
An yi gyara a tsarin tsaro
Sufeto Janar na yan sandan, IGP Alkali Usman Baba ya cire mataimakin Sufeto Janar na yan sandan, DIG Joseph Egbunike a matsayin shugaban tawagar tsaro na zaben gwamnan Anambra yan sa’o’I kafin zaben.
Kakakin rundunar yan sandan kasar, CP Frank Mba, ya tabbatar da cewar an sauyawa DIG Egbuike wurin aiki, amma bai bayyana dalilin cire babban jami’in wanda ya kasance dan asalin jihar Anambra ba.
Sai dai kuma, kakakin shiyar, Princess Nkeiruka Nwode, ta ce DIG Egbunike bai yi murabus ba kamar yadda aka rahoto a wasu bangarori.
Rahotun Jaridar Legit