Type Here to Get Search Results !

Jaruma Rahama MK, matar gwamna a fim din Kwana Casa'in ta yi auren sirri


Ana tsaka da more shiri mai dogon zango na Kwana Casa’in sai aka wayi gari da batun auren sirri da wata jarumar fim din ta yi.

Jaridar Dimokardiyya ta ruwaito cewa, Rahama MK, wacce ta fito a matsayin matar Gwamna Bawa Mai Kada ta yi auren ta a ranar Asabar 6 ga watan Nuwamba.


Rahotanni sun nuna yadda aka yi shagalin bikin a gidan su da ke cikin garin Kano cike da sirri don ba kowa ya sani ba.

Tuntuni an samu labari a kan batun auren jarumar amma ba ta fadi lokaci da kuma wanda za ta aura ba, hakan ya sa mutane su ka dinga mamaki.

Yayin da wakilin jaridar Dimokuradiyya ya bukaci jin ta bakin jarumar ta bayyana cewa:

“Dama na shaida cewa zan yi aure tun kwana 3 da su ka gabata, kuma ga shi Allah ya tabbatar kuma ya cika min buri na.”
Ta kara da addu’ar Allah ya ba ta haihuwa kuma ta yi fatan mutuwa a dakin mijin ta.

Batun fina-finai kuma ta ce za ta ci gaba da fitowa a shirin Kwana Casa’in, amma sauran babu tabbas.

Maryam Booth ta sa an kwamushe matashin da ya yada labarin ta na neman miji

Legit Hausa

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies