An bindige wani Birgediya Janar har lahira a harin kwantan baunan da yan ta'adda Daular Musulunci a yammacin Afrika ISWAP suka kaiwa jami'an Soji a jihar Borno, rahoton DailyTrust.
Sabanin shi an hallaka jami'an Sojoji hudu a harin kwantan bautan da ya auku a Bulguma, kusa da garin Askira, a karamar hukumar Askira Uba.
An tattaro cewa jami'an 28 Task Force Brigade, Chibok, sun tashi daga barikinsu don kaiwa Sojin dake Askira dauki amma aka bude musu wuta.
Mun kawo muku cewa 'Yan ta'addan ISWAP sun yi musayar wuta da sojoji a wani sansanin soja da ke karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.
Wasu mazauna sun ce sun hango mayakan na ISWAP a cikin wani dogon ayarin motocin bindigu a hanyar Ngude zuwa Askira, da sanyin safiyar yau.
Adamu Saleh ya shaida wa The Sun cewa: “Al’amarin ya yi muni amma ‘yan ta’addan sun janye a yanzu.”
Mazauna sun yi ikirarin cewa sun kai rahoton zirga-zirgar 'yan ta'addan ga jami'an tsaro amma ba a dauki wani mataki ba kafin wannan mummunar kungiyar ta afkawa garin Askira bayan sa'o'i. Source: Legit Nigeria
Reported by ISYAKU.COM
Domin samun labaran mu ta Whatsapp kai tsaye Latsa Link a kasa
https://chat.whatsapp.com/
Domin Tuntubar mu ko aiko Labari LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu LATSA NAN
Shafin mu na Facebook facebook.com/isyakulabari
Shafin mu na Twitter twitter.com/isyakulabari