Ire-iren Mata 3 da suka haramta a Aura, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa


A wannan karo, Malam ya yi bayani kan Matan da suka haramta a aura a Musulunci Matan da suka haramta a aura a musulunci sun kasu kashi uku: Na ɗaya waɗanda suka haramta a aure su har abada, 

Na biyu waɗanda aka haramta a aure su, bisa wani dalili da zai iya gushewa idan ya gushe zuwa wani lokaci za a iya auran su idan kuwa dalilin yana nan babu damar auran su. 

Na uku waɗanda aka haramta auran su bisa wani dalili da ya bijiro. 


Idan muka ɗauki kashi na farko wato waɗanda aka haramta auran su har abada, babu wani dalili da zai sa a aure su. Sun kashi kashi huɗu : 

Na ɗaya waɗanda aka hana auran su saboda kusanci na dangantaka ta jini 

1. Mahaifiya da dukkan kakanni na wajan uwa da na wajan uba. 

2. Ƴa, mutum ba zai auri ƴarsa ba ko jikarsa, duka na wajan ɗa namiji da na wajan Ƴa mace. 

3. Ƴar'uwa babu aure tsakanin mutum da Ƴar'uwarsa, duka shaƙiƙiya, li-abbiya li-ummiya. 

4. Ƴar'uwar mahaifi, babu aure har abada tsakanin mutum da Ƴar'uwar mahaifinsa wacce suke uwa ɗaya uba ɗaya, da wacce suke uba ɗaya da wacce suka uwa ɗaya. 

5. Ƴar'uwar mahaifiya shaƙiƙiya da liabbiya da li'ummiya. 
6. Ƴaƴan ɗanuwanka, gaba ɗaya, shaƙiƙi li'abbi da li'ummi. 

7. Ƴaƴan Ƴar'uwarka da kuke uba ɗaya ko uwa ɗaya ko uwa ɗaya uba ɗaya. Waɗannan sune kashin farko waɗanda suka haramta mutum ya aure su har abada idan kuwa mutum ya auri ɗaya daga ciki da gangan hukuncin kisa ne a musulunci. 

Kashi na biyu sune: 


Waɗanda suka haramta saboda dalili na shayarwa idan jariri ya sha nonon mace yana yaro 

Wannan matar ta zama uwar sa ta shayarwa, don haka yadda danginsa da muka lisaafa suka haramta a gare shi ita ma haka abin yake 

1. Mahaifiyarka ta shayarwa da dukkan kakanni na wajan uwa da na wajan uba. 

2. Ƴar , matar da ta shayar da kai ba za ka auri ƴartaba ko jikarta, duka na wajan ɗa namiji da na wajan Ƴa mace. 

3. Ƴar'uwar ka ta shayarwa aure tsakanin mutum da Ƴar'uwarsa, duka shaƙiƙiya, liabbiya liummiya.wacce suka sha nono tare ta haramta a gare shi. 

4. Ƴar'uwar mijin matar da ta shayar da kai nono , babu aure har abada tsakanin mutum da Ƴar'uwar mahaifinsa na shayarwa wacce suke uwa ɗaya uba ɗaya, da wacce suke uba ɗaya da wacce suka uwa ɗaya. 

5. Ƴar'uwar mahaifiyarsa ta shayarwa, shaƙiƙiya da liabbiya da liummiya. 

6. Ƴaƴan ɗanuwansa, na shayarwa gaba ɗaya, shaƙiƙi li'abbi da li'ummi. 

7. Ƴaƴan Ƴar'uwarka ta shayarwa da suke uba ɗaya ko uwa ɗaya ko uwa ɗaya uba ɗaya. 

Sai kashi na uku, sune waɗanda suka haramta saboda dalilin surukuta, su kuma su huɗu ne 

1. Babar matarka 

2. Matar da ɗanka ya aura ya sake ta. 

3.Matar da babanka ya aura ya sake ta. 

4 Ƴar matarka wato agola wacce ka tare da mahaifiyar ta. 

Waɗanan su huɗu sun haramta ne bisa dalilin surukuta. 

WAƊANDA SUKA HARAMTA A HAƊA SU A ƘARƘASHIN MIJI ƊAYA. 


Akwai kuma waɗanda dalilin haramta su shine ba a haɗa su guri guda, sai idan ba ɗayar ake auran ɗayar sune: 

1. Haɗa tsakanin mace da ƴar'uwarta wacce suke uwa ɗaya uba ɗaya, ko uba ɗaya ko uwa ɗaya. 

2. Haɗe mace da ƴar'uwar mahaifin ta a ƙarƙashin miji ɗaya. Idan mutum ya auri mace kuma daga baya sai ya auri ƴar'uwar mahaifin ta ko mahaifiyar ta ko ƴar'uwar, wannan auran na biyu ya ɓaci, sai a warware shi, a tsaya akan na farkon. 

3. Haɗa mace da ƴaruwar mahaifiyar ta ƙarƙashin aure ɗaya miji ɗaya. 

Source: Legit 
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN