Rundunar 'yan sandan Nigeria, a Jigawa ta yi nasarar kama wani mutum mai shekaru 48 da ake zargin hatsabibin dilalin miyagun kwayoyi ne.
An kama shi ne a karamar hukumar Hadejia da ke jihar ta Jigawa kamar yadda ya zo a ruwayar The Nation.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa ASP Lawan Shiisu, mai magana da yawun rundunar yan sandan Jigawa, ne ya sanar da hakan a ranar Juma'a a Dutse, babban birnin jihar.
Yadda aka kama wanda ake zargin Shiisu ya ce tawagar wasu 'yan sanda ne suka kama wanda ake zargin a ranar 15 ga watan Nuwamba misalin karfe 12.30 na rana.
Ya yi bayanin cewa tawagar, yayin da suke sintiri a Hadejia sun kama wanda ake zargin a Gundun Sarki Quaters.
Abin da aka kwace a hannunsa
Kakakin yan sandan ya kara da cewa an samu kwallabe 43 na wasu abubuwa da ake zargin muggan kwayoyi ne a hannun wanda ake zargin.
Ya ce za a gurfanar da shi a gaban kotu idan an kammala bincike. Shiisu ya kara da cewa an kama wasu mutane shida da ake zargin bata gari ne a karamar hukumar Kiyawa.
Ya ce an kama su ne bayan kai samame a mabuyar bata gari da kauyen Balago a ranar 16 ga watan Nuwamba misalin karfe 7 na yamma.
Da an kammala bincike suma za a gurfanar da su a kotu.
Legit Nigeria