Gwamnonin Najeriya sun ja daga da Ministan shari'a Malami saboda tsare gida kan wasu makudan kudi


Wata takaddam ta barke tsakanin kungiyar gwamnonin Najeriya da Ministan Shari'ar kasar kan kudin Paris Club da aka yafewa kasar.

Rashin jituwar tana da nasaba ne da umarnin da Ministan Shari'ar kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubukar Malami ya bayar na biyan wani bangaren na kudin ga kwararrun da suka shiga tsakani domin kungiyar Paris Club ta yafe wa kasar bashin da ta ciyo daga hannunta a shekarun da suka gabata.

Sai dai gwamnonin jihohi 36 a karkashin inuwar kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) sun caccaki Abubakar Malami kan wannan mataki saboda a cewarsu batun na gaban kotu.

Sanawar da gwamnonin suka fitar da ke dauke da sa hannun kakakin kungiyar ta NGF, Abdulrazaq Bello Barkindo ta ce akwai lauje cikin nadi game da umarnin da Malami ya bai wa Ministar Kudi ta kasar da ta biya kudin.

Abin da ya haifar da takaddamar

A ranar 5 ga watan Nuwamba wata kotu a Abuja ta hana gwamnatin tarayya cire dala miliyan 418 daga asusun ajiyar kudi na jihohin 36 da ke kasar.

Kudin da ake zargin kwararrun suna bin gwamnati kan aikin da suka yi lokacin tattaunawar neman kungiyar Paris Club ta yi wa Najeriya yafiya, ya kasance tushen takaddama tsakanin bangarorin gwamnati uku.

Tun farko Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya nuna rashin jin dadinsa kan rade-radin da ke cewa yana aiki ne ba tare da bin kai'da ba kan basussukan da suka taso game da kudaden da aka rika cirewa da kuma mayar wa jihohi da kanana hukumomi daga kudaden na Paris Club.

A sanarwar da kakakin ministan Umar Jibril Gwandu ya fitar, Malami ya nanata cewa an cire kudin ne bayan hukunce-hukuncen kotu hudu da aka yi a shekarun 2014, 2015, 2017 da kuma 2019.

Sai dai gwamnonin sun ce umarnin da ministan ya bayar ya sabawa muradun 'yan Najeriya kuma sun nuna shakku kan yawan kudin da kwararrun suke son a biya su.

Sun ce akwai alamar tambaya game da shawarar da Malami ya yanke ta goyon bayan a biya su dala miliyan 418 daga asusun gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi .

Gwamnonin sun ce : "Ya kamata babban lauyan gwamnatin tarayya ya kasance babban mai sasatanwa a duk al'amuran da suka shafi 'yan Najeriya, musaman talakawan kasar nan."

"Hanzarin da aka yi wajen fitar da sanarwar tun kafin a gabatar wa ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya hukuncin da kotu ta yanke a ranar 5 ga watan da muke ciki da ya hana gwamnatin tarayya cire kudin, ya nuna akwai dangantaka ta musamman tsakanin ofishin ministan da kuma kwararrun," in ji su

Sun kuma ce Ministan Sharia'ar ya kasa bayar da cikakken bayani a kan dalilin da ya sa kotu ta yanke hukunce-hukunce hudu a baya.

Sai dai Abubakar Malami ya ce biyu daga cikin hukunce-hukuncen suna da nasaba da sharudan sasantawa da aka cimma lokacin da kungiyar gwamnoni ta shigar da kara a shekarun 2017 da 2019.

Ya kuma ce sauran biyun wata babbar kotu ce ta yanke a shekarar 2013.

A cewar ministan "Abin mamaki shi ne daga 2013 - 2021 kungiyar gwamnoni ko ALGON ba su ga ya dace su kalubalanci ko aiwatar da wadannan hukunce hukuncen ba."

Sai dai gwamnonin sun musanta haka ko da yake sun amince cewa ba su shigar da kara a kan lokaci ba amma daga bisani sun kalubalanci hukunce-hakuncen a kotuna daban- daban.

A shekarar 2005 ne kasashen duniya masu bayar da bashi karkashin kungiyar Paris Club suka yafe wa Najeriya bashin da suke binta.

Kasashen sun yi haka ne domin kasar ta yi amfani da kudin don samar da ababen more rayuwa ga al'ummart

BBC Hausa
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN