Gaskiya ta fito: Dalilin da yasa wajibi shugaba Buhari da Arewa su goyi bayan Bola Tinubu a 2023


Ga dukkan alamu komai na tafiya kamar yadda aka tsara shi kuma ake tsammani game da takarar Asiwaju Bola Tinubu gabanin babban zaben 2023. 

Guardian ta gano cewa akwai ikirarin ko shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da yankinsa na Arewa a ɗaure suke, wajibi su goyi bayan takarar Tinubu. Kungiyar matasan APC (APCN4NYA), ita ce ta bayyana haka ranar Laraba 17 ga watan Nuwamba 2021. 

Meyasa kungiyar ta yi wannan ikirarin? A wata sanarwa da sakatare janar na kungiyar APCN4NYA, Oludayo Ogunjebe, ya fitar, yace gudummuwar da jagoran APC ɗin ya bayar, ta fi karfin a yi watsi da ita. 

Oludayo ya kara da cewa Tinubu ba wai mamban jam'iyya bane kaɗai, shine ƙashin bayan jam'iyyar APC mai mulki. Ya kuma yi ikirarin cewa a baki ɗaya yankin kudancin Najeriya, babu wanda ya cancanta, ya dace ya gaji Buhari kuma ya jagoranci Najeriya a 2023. Abinda zaɓen 2023 ke nufi a APC?

 Bugu da ƙari, Oludayo yace zaɓen 2023 zai zama tamkar yaba kyauta ne da tukuici ga Tinubu, domin saka masa da goyon baya kan gudummuwar da ya bayar. Sakataren yace: "Yan Najeriya sun san cewa in banda ni'imar da Allah ya mana da Asiwaju Tinubu, ina da tabbacin da yanzun ba jam'iyyar mu bace take mulki." 

"Saboda haka a wurin mu, wannan lokaci ne da zai samu sakayya daga yan uwa daga dukkan yankunan da muke da su, mu goya masa baya ya jagoranci ƙasar nan domin cika kyakkyawan burinsa." 

"A wurin mu, ba karamin babbar asara bace ninki biyu, idan aka ce Bola Tinubu bai samu damar gadar shugaba Buhari a 2023 ba." 

Source: Legit Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN