Gaskiya ta fito: ASUU ta magantu kan nadin da aka yi Pantami a matsayin Farfesa


Kwamitin binciken kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ya wanke hukumomin jami’ar fasaha ta tarayya da ke Owerri (FUTO) daga cece-kucen da ake yi na nadin ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ibrahim Pantami, a matsayin Farfesa na Tsaron Intanet.

Jami'ar ta ce ta bi ka'idojin da suka dace kuma ta gabatar da wallafe-wallafen Pantami don tantancewa ga masu tantancewa na waje sannan kuma ta kafa ka'idar farko don nada shi Farfesa na Tsaron Intanet.

Kwafin rahoton mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin Farfesa MS Nwakaudu da wasu mambobi hudu ya bayyana irin matakan da jami'ar ta bi wajen nada Pantami Farfesa.

Daily Sun ta ruwaito rahoton na cewa:

“Daga binciken da muka yi da shaidun da ke gaban kwamiti, mambobin na da ra’ayin cewa nadin Dr Isa Ibrahim a matsayin Farfesa a fannin tsaro ta Intanet ta hanyar Majalisar gudanarwa ta FUTO ta bi tsarin da ya dace.

"Kwamitin ya ba da shawarar ya kamata mahukuntan jami'ar cikin gaggawa su dauki matakan da suka dace, ciki har da na shari'a, a kan wadanda suka yi kokarin jawo zubar kima da martabar FUTO."
Rahoton ya yi nuni da cewa, sakamakon wasu kura-kurai da aka samu kan nadin Pantami a matsayin Farfesa a Makarantar Fasahar Bayanai da Sadarwa (SICT), kungiyar ASUU ta FUTO a ranar 22 ga Satumba, 2021 ta kafa kwamitin binciken.

A cewar rahotanni, an ba da umarnin a cikin kwanaki bakwai a tabbatar ko an aiwatar da tsarin da ya dace wajen nadin Pantami a matsayin Farfesa na Tsaron Intanet ta Majalisar Mulki ta FUTO, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce shugaban SICT ya tantance wallafe-wallafen da ayyuka masu inganci ta amfani da ka'idojin FUTO na nadawa da habakawa kuma ya kafa ka'idar farko don a nada shi Farfesa na Tsaron Intanet.

Ya kara da cewa an gabatar da kaidar farko ga kwamitin tantance ma'aikata da kara girma (ASAPC-Professorial) kuma kwamitin ya tattauna batun tare da ba da shawarar hakan don amincewa daga majalisar FUTO.

PR Nigeria tace Ministan ya na cikin mutane bakwai da suke matsayin mataimakin Farfesa da suka tsallaka zuwa Farfesa a jami’ar tarayya ta Owerri.

Jami’ar fasahar FUTO da ke jihar Imo ta dauki wannan matakin ne a zama na 186 da ta yi wanda ya gudana a ranar Juma’a 20 ga watan Agusta, 2021.

Source: Legit

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN