EndSARS: Bayan shekara 1, bincike ya tona abin da ya faru a Lekki, an zargi Soji da kisan kiyashi


Kwamiti na musamman da gwamnatin jihar Legas ta ba alhakin binciken abin da ya faru a lokacin zanga-zangar #EndSARS ya kammala aikinsa.

VOA Hausa tace binciken kwamitin ya bada tabbacin cewa jami’an tsaro sun kashe wasu daga cikin wadanda suka yi zanga-zanga a kofar shiga Lekki.

Kwamitin da Alkali Doris Okuwobi ta jagoranta ya tabbatar da cewa sojoji sun buda wuta ga masu zanga-zanga a bakin kofar shiga wannan unguwa a Legas.

Hakan ya sa tsautsayi ya yi sanadiyyar mutuwar wasu da suka fito zanga-zangar lumana domin yin Allah-wadai da zaluncin jami’an ‘yan sanda a Najeriya.

Matasan sun zargi dakarun SARS da zalunci, suka ce su na tare mutanen da aka gani dauke da komfuta, ana jifarsu da zargin damfara, har a harbi wasunsu.

Kwamiti ya gabatar da dogon rahoto

Wannan rahoto mai shafuka sama da 300 da kwamitin binciken ya gabatar, ya bayyana yadda jami’an tsaro suka aukawa masu zanga-zangar ta lumuna.

Rahoton yace jami’an tsaron da ake zargi da laifi sun hada da sojojin kasa da dakarun ‘yan sanda.

Ta'adin da jami'an tsaro suka yi a Lekki

Jami’an tsaro sun harbi Bayin Allah barkatai a wajen wannan zanga-zanga, bayan haka suka dauke gawawwakin da harsasan bindiga, domin birne sawunsu.

Kwamitin yace a ranar 20 ga watan Oktoban 2021, sojoji sun buda wuta ga mutanen da ba su rike da wani makami sai tutar Najeriya, suna rera taken kasarsu.

Wannan kwamiti na musamman ya zargi jami’an tsaro da hana bada motocin asibiti, a taimakawa masu rauni, a karshe ya ba gwamnati shawarwari.

Shawarar da MURIC ta ba masu zanga-zanga

A lokacin da aka ruguza dakarun SARS saboda zargin da ake yi mata, kungiyar nan MURIC ta yi magana ta na kiran a janye zanga-zangar #EndSARS da ake yi.

MURIC mai wayar da kan jama’a kan hakkokin musulmai, ta gargadi masu wannan zanga-zanga da cewa su yi hattara da mugun nufin wasu da suka shiga rigarsu.

Legit Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN