Dubun wasu tsagerun yan bindiga da suka addabi jihohin Sokoto da Zamfara ya cika


Haukumar tsaro (NSCDC), ranar Laraba, ta sanar da kame wasu tsagerun yan bindiga guda huɗu a jihar Sokoto. Channelst tv ta ruwaito cewa waɗan da ake zargin mambobin manyan ƙungiyoyin yan bindiga ne da suka addabi jihohin Sokoto da Zamfara. 

Jami'ai sun damke mutanen ne bisa zargin hannu a garkuwa da manyan mutane, fashi da makami, satar dabbobi da kuma kashe mutane a wasu yankunan waɗan nan jihohi biyu. 

An gayyaci wani babban mutum Kwamandan jami'an NSCDC reshen jihar Sokoto, Mohammed Saleh-Dada, yace wasu daga cikin mutanen da aka damke yan leken asirin yan bindiga ne. 

A cewar kwamandan hukumarsu ta gayyaci wani babban mutum da ake zargin yana da alaƙa da ɗaya daga cikin mutanen da aka kame. 

Yace: "Mun gayyaci wani sanannen mutum a yankin karamar hukumar Dange/Shuni, jihar Sokoto, bisa zargin yana da wata alaƙa da mutum daya da ake zargi." 

A wani labarin kuma Miyagun yan bindiga sun kai wani mummunan hari Kaduna, sun kashe mutane 

Source: Legit Newspaper 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN