Duba garin da babu wanda ya kammala furamare a Kano da abin da aka yi masu


A jihar Kano da ke arewacin Najeriya, al`ummar garin Shara da ke karamar hukumar Sumaila ta kwana tana murna, sakamakon gina mata makarantar furamare da gwamnati ta yi.

Ana da akalla mutum 3000 a garin, amma babu ko da mutum daya da ya kammala karatun furamare saboda wahalhalun da suke fuskanta wajen zuwa wata makaranta da ke nesa da garin nasu.

Kungiyar bunkasa fasarar sadarwa da cigaban al`umma, wato CITAD ita ce ta taimaka ta hanyar bibiyar mahukunta wajen ganin an samar da makarantar.

Daliban makarantar furamaren garin na Shara sun cika da farin cikin samun sabbin ajujuwan karatu guda biyu da ofishin hedimasta, bayan sun shafe shekaru suna daukar karatu a gindin bishiya.

Mallam Muhammad Labiru Musa shi ne shugaban kungiyar iyayen yara da malaman makaranta ta Shara, ya shaida wa BBC cewa rashin irin wannan daddadan yanayi na karatu na cikin dalilan da suka hana al`ummar garin mai mutum fiye da dubu uku yin karatun zamani, don haka babu ko da mutum daya da ya kammala furamare.

''Tun lokacin da muke kanana akwai wani gari can kudu da mu mai suna Matigwai, akwai jeji da kwari idan damuna ta zo babba bai isa haurawa ba saboda birai kai har da ungulu sun isa hana ka zuwa makarantar,'' in ji Malam Muhammadu.

Shi ma Malam Kabiru Umar Sitti, wanda shi ne malami daya tilo da ake da shi a garin na Shara, ya shaida wa BBC cewa a wasu lokutan idan yara na daukar karatu a gindin bishiya, haka za a zo ana sissikar kaikayi ko hatsi wanda dole take sanyawa yaran su hakura da karatun, amma yanzu wadannan azuzuwa da aka yi musu za su bayar da kwarin gwiwar ci gaba da koyar da daliban.

Tuni dai wasu daga cikin daliban suka fara jin cewa burinsu na rayuwa zai cika, inda wata daliba mai suna Zahira Musa ta ce a baya suna karatu a gindin bishiya, kuma da zarar damuna ta tsaya sai dai hakuri. Ta ce wadannan azuzuwa da aka gina musu sun ba ta kwarin gwiwar zage damtse har sai burinta ya cika na zama jami'ar kiwon lafiya nan gaba.

Cibiyar bunkusa fasahar sadarwa da cigaban al`umma, wato CITAD, ita ce ta yi ta kai gwauro da mari wajen nuna wa duniya matsalar da ke damun al`ummar Shara ta rashin makaranta ta hanyar bin hukomomin da shugabannin siyasa, har a karshe maganar ta kai ga share musu hawaye.

Shugaban karamar hukumar Sumaila, wanda mai taimaka masa, Alhaji Nasiru Ibrahim Sitti, ya tabbatar da cewa Gwamna Ganduje ne ya ji korafin mutanen garin. Za kuma a kai musu kayan koyo da koyarwa da kujeru har da karin malamai domin inganta wannan makaranta.

A jihohin arewacin Najeriya da dama, akwai irin wannan al`ummar masu yawan gaske, wadanda abu kalilan mahukunta za su yi su sauya musu rayuwa. Kididdiga ta nuna yawancin yara mata da maza ba sa samun damar yin ilimin boko a arewacin Najeriya, ko dai saboda rashin wadatar makarantu, ko malamai ko kuma cire yara mata a yi musu aure cikin kankantar shekaru

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN