Daga rigima a gida, wata mata tayi wa Mai gidanta wanka da ruwan ‘Acid’


Wata mata da aka bada sunanta a matsayin Becky ta shiga cikin matsala a sakamakon zarginta da laifin watsawa mijinta ruwan asid a jiki.

Jaridar Daily Trust tace wannan mummunan abin ya faru ne a birnin Benin, a jihar Edo.

Becky ta watsawa mai gidan na ta ruwan asid mai dafi ne a sakamakon fadan da suka yi bayan sabani ya shiga tsakaninsu a gidansu da ke jihar Edo.

Rahoton yace Becky ta dade tana kuka da mijin na ta mai suna Odion, wanda har ta taba kai shi gaban ‘yan sanda domin su dauki mataki a kan shi.

Jami’an ‘yan sanda sun ba matar hakuri a wancan lokaci, ta nemi ta je ta sasanta da mijinta.

Kaddara ta riga fata

An fahimci cewa ‘yanuwan ma’auratan suna neman su yi masu sulhu ne, sai kwatsam aka ji matar ta watsawa mijinta asid a karshen makon jiya.

Majiyar tace da makwabta suka ji Odion yana ihu, sai suka garzayo gidansu domin kawo masa agaji, sai kurum aka same shi a kwance, yana ta birgima.

Matar da yayi wannan abin ta shiga hannun hukuma, tuni ‘yan sandan garin Benin suka cafke ta. Amma ‘yanuwan mamacin su na cewa matar ta tsere.

Da aka tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar a ranar Laraba, 17 ga watan Nuwamba, 2021, ta bayyana cewa za ta fitar da cikakken jawabin kan da ya auku.

Odion ya mutu a asibiti

Wani rahoto daga Express News yace Odion ya rasu bayan ya yi fama da ‘yar jinya. Magidancin ya rasu ne a asibitin koyar da aikin likitoci na jami’ar Benin.

‘Yar uwar marigayin, Esohe Fidelis tace dama matar tace sai ta ga bayan Odion, ga shi nan tayi nasarar kashe shi, ya mutu ne sa’a 12 bayan abin da ya farun.

Legit Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN