An yi artabu tsakanin yan bindigan daji da zaratan yan kishin kare kasar Zuru, Yan sa kai ranar Talata, lammari da ya yi sanadin mutuwar Yan sa kai guda uku da kuma yan bindiga guda hudu a kauyen Yan Kuka wanda ke rikon kasar Tadurga a karamar hukumar Zuru da ke kudancin jihar Kebbi.
Rahotanni sun ce yan bindigan wadanda ke tafe a kafafunsu, sun gamu da turjiya daga Yan sa kai yayin da suka yi kokarin shiga kauyen Yar Kuka, sakamakon haka aka yi bata kashi da ya yi sanadin mutuwar Yan sa kai guda uku.
Sai dai daga bisani Yan sa kai sun yi gangamin da ya kai su ga nassarar tunkarar Yan bindigan kuma suka bi su har cikin daji suka kashe Yan bindiga biyar nan take, kuma suka raunata da dama sakamakon haka ya sa Yan bindigan suka watse da gudu a cikin daji.
Kazalika mun samo cewa tuni aka tura soji da jami'an yan sanda a wajen da lamarin ya auku, ciki har da manyan jami'an tsaro.
Rubuta ra ayin ka