Wasu tsagerun yan bindiga sun kai hari gidajen Malaman jami'ar Abuja (UniAbuja) cikin daren Talata, 2 ga watan Nuwamba 2021 kuma sun yi awon gaba da mutane. Legit Hausa ta tattaro cewa yan bindiga sun dira gidajen ne dake unguwar Giri, hanyar zuwa tashar jirgin sama Gwagwalada, Abuja.
Hakazalika Jami'ar ta bayyana cewa tuni an tura jami'an tsaro domin tabbatar da tsaro a wajen. Jami'ar ta sanar da wannan hari a shafinta na Facebook.
Tace: "Wasu yan bindiga sun kai hari gidajen ma'aikatan jami'ar Abuja da safiyar nan. Tuni mun tura jami'an tsaro domin kare mutane."
Mutum nawa aka sace? Jami'ar ta bayyana cewa an yi awon gaba da ma'aikatan jami'ar akalla mutum hudu da iyalansu. "Muna sanar da cewa an sace ma'aikatanmu hudu da yaransu. Muna kokarin tabbatar da cewa sun kubuta. Yau dai ba dadi," jawabin ya kara.
Source: Legit.ng