Da duminsa: Yadda bala'i ya fada wa yan bindigan daji aka kashe kasurgumin dan bindiga Damana da yaransa fiye da 100


Bayanai na ƙara fitowa fili a kan faɗan cikin gida da aka samu tsakanin 'yan fashin daji, da ya zama sanadin mutuwar wasu daga cikinsu a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Wasu mazauna yankin wadanda ke da masaniyar abubuwan da suka faru sun shaida wa BBC Hausa yadda wani rikici tsakanin 'yan fashin dajin ya zama ajalin wani ƙasurgumin ɗan fashin da ya addabi sassan jihar da hare-hare da satar mutane don neman kuɗin fansa.

Rahotanni sun ce cikin laifukan da ake zargin Damina, da aikatawa kafin a kashe shi, har da ƙona wata mata da ranta.

Mallam Nuhu Ɗan Sadau, wani mutumin garin Ɗan Sadau ne mai maƙwabtaka da dajin da 'yan fashin ke samun mafaka, ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne makonni uku da suka gabata.

"Yanzu Allah ya taimake mu duk inda aka ji fashin 'yan bindiga daya, biyu, uku, sai ka ji wani abu ya faru tsakaninsu suna kashe junansu," a cewarsa.

Ya ce: "A baya-baya nan mun samu raguwar yan fashin daji fiye da 150 wajen rabon ganima da wasu abubuwa, sai su kama fada, su kashe junansu, shi ya kawo labarin da kuke ji cewa Dogon Gide ya kashe Damina," In ji shi

Yadda aka kashe Damina

A cikin bayanan da aka samu kan kashe-kashen baya-bayan nan na 'yan fashin daji, labarin kisan Damina da yaransa sama da 100 ya fi jan hankalin jama'a.

Bayanai sun kuma ce fadan da suka yi na da nasaba da satar shanun Dogo Gide da ake zargin Damina ya yi a yankin da Dogo Gide yake da tasiri.

Mallam Nuhu Ɗan Sadau ya ce:"Damina ya samu labarin Dogo Gide ya fita daga yankin da yake zaune, sai Damina ya saci hanya ya shiga hurumin Dogo Gide, ya kwashi shanu kuma ya kori al'ummar da ke zama a wurin.

"Wadannan mutane su suka hada shi da Dogo Gide har ya kore shi daga yankin, saboda haka yanzu su ma sun bar wurin kuma sai ya ga yadda za su debi amfanin gona, idan suna so sai sun ba da miliyan shida", in ji shi

Bayanan sun kuma ce sai da Damina ya sa wa mutanen haraji, ya kuma wakilta wadanda za a bai wa kudi har miliyan shida.

Sun kuma ce bayan komawarsa sai Dogo Gide ya samu labari kuma ya bi sahu, shi ma ya kashe na kashewa, ya kwaso shanunsa da aka sace kuma shi ma ya sato na Damina.

Mallam Nuhu Ɗan Sadau ya kara da cewa:"An sace masa shanu fiye da 100, shi kuma ya sato sama da 300 ,to shi ne kuma Damina ya shirya ya biyo, shi kuma Dogo Gide da ya yake shiryayyen dan fashin daji ne ya shirya masa harin kwantar bauna, ko da zai biyo da tawagarsa sai da ya shigo tsakiyar dajin da ake kira Farin Ruwa da ke kusa da garin Ruwan Tofa. A wannan daji suka yi ba-ta-kashi, suka kashe mafi yawan yaran da Damina ya zo da su."

A cewarsa: "Ni na ga wanda ya ga bindigar Damina, da babur dinsa da jakar makaminsa domin an kai su wani kauye da ake kira Chilinda."

Bayanai sun ce Damina ya tafi da raunuka kuma an samu labarin ya bulla a kauyen Farin Ruwa inda a nan ya gamu da ajalinsa bayan 'yan kato da gora sun sanar da mazauna kauyen wadanda suka taru suka sassare shi

Sai dai kawo yanzu babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabattar da wannan labari kuma mahukunta ba su ce komai ba a kan batun ba.

Amma a baya bayan nan an kashe rikakkun 'yan fashin daji, cikinsu har da Nasiru Kachalla da Auwal Daudawa da sauransu.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN