Da duminsa: Wata daliba a Katsina ta kwankwadi piya-piya saboda saurayinta ya rabu da ita, duba abin da ya biyo baya


Wata dalibar aji uku a jami'ar Umaru Musa Yar’adua, jihar Katsina ta kwankwandi gorar sabulun tsaftacce hannu da piya-piya bayan saurayinta ya rabu da ita. 

21st CC ta ruwaito cewa majiyoyi sun bayyana sunan yarinyar matsayin Ummi, kuma yar jihar Kaduna ce amma tana da yan uwa a Katsina. 

Wata daliba da ta bukaci a sakaye sunanta tace:

 "Da daren nan (Juma'a) shi (saurayin) ya zo dakin kwanan mata ya fadawa Ummi ya rabu da ita. 

Bamu san ainihin abinda ya hadasu ba, ko wadanda ke daki daya da Ummi basu san takamammen abinda ya hadasu ba." 

Sai ta koma daki ta dauki hand sanitizer da pia pia don fushin abinda yayi mata." 

Saurayin wanda sunansa bai bayyana ba har yanzu shima dalibi ne a jami'ar UMYUK ne. Wata majiyar ta bayyana cewa shan piya-piyan ke da wuya ta fara amai kuma ta sume. 

Tace: 

"Abokan kwananta sun sanar da jami'ar kai tsaye kuma aka turo motar asibiti don kai ta asibiti." 

Source: Legit 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN