Da duminsa: Sojoji sun kashe yan bindiga da yawa a hanyar Kaduna-Abuja


A wani martani na musamman, jami'an tsaro sun aika dandazon yan bindiga lahira, waɗan da suka addabi matafiya a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa jami'an tsaron sun ɗauki wannan matakin ne bayan umarnin da shugaba Buhari ya baiwa hafsoshin tsaro.

A wani hoton bidiyo da jaridar PRNigeria ta samu, ya nuna gawarwakin yan bindigan sama da goma.

Wata majiya daga jami'an tsaro, ya bayyana cewa ana cigaba da jibge jami'ai da suka haɗa da sojoji, yan sanda, da jami'an fasaha a wasu kauyuka dake kan babbar hanyar.

Wace nasara aka samu zuwa yanzu?

Jami'in yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Tun kafin shugaban ƙasa ya bada umarni aka kara jibge jami'an tsaro amma umarnin yasa ak kara turo jami'ai da dama, da kayan aiki yakar yan bindigan."

"Zuwa yanzun mun kashe sama da yan bindiga 12 waɗan da suka yi kokarin tserewa da suka ga sojoji sun fara shawagi."

"Mafi yawan yan bindigan da muka kashe suna da hannu a sace matafiya na kwanan nan domin mutanen yankin sun gane fuskokin gawarwakin."

Wane uamrni shugaba Buhari ya bayar?

Legit.ng Haura ta rahoto muku cewa a ranar Alhamis, shugaban kasa Buhari ya umarci hafsoshin tsaro su kawo karshen yan bindiga da yan ta'addan da suƙa hana zaman lafiya a Najeriya.

Shugaban ya ba su wannan umarnin ne a taron majalisar koli kan tsaro, ya kata da cewa kada su rintsa har sai yan Najeriya sun iya bacci cikin kwanciyar hankali.

Kazalika, shugaba Buhari ua umarci hukumomin tsaro su ƙara zage dantse wajen shawagi a kan hanyar Kaduna-Abuja domin ceto mutanen da aka sace.

A wani labarin na daban kuma

Source: Leg

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN