Da duminsa: Maciji ya sari Jami'ar soji a cikin ban dakin gidanta ta mutu, duba yadda ta faru


Wata jami'ar hukumar mayakan saman Najeriya, Lance Kofur Bercy Ogah, ta gamu da ajalinta cikin ban daki yayinda macijiya ta cijeta a gidanta.

Jami'ar ta fuskanci cizon macijiyar ne yayinda take biyan bukatarta a bayin gida cikin barikin Sojin NAF Base dake Abuja.

Punch ta ruwaito cewa bayan cizon, Kofur Ogah ta kwashe yaran dake gidanta kuma ta kaisu wajen makwabta sannan ta garzaya asibitin Nigerian Air Force hospital amma lokaci ya yi.

A rahoton, wannan abu ya auku ne da safiyar ranar Juma'a.

Wata majiya, a cewar Punch, ta bayyana cewa:

"Za ka tarar da muggan dabbobi irin wannan a barikin. Mazauna na gamuwa da macizai sosai."

"An sanya magunguna a gidajen kwanan nan amma an tsallake nata saboda ba ta nan lokacin. Da yiwuwan macijin ya boye a bayinta."

"Bayan cizon macijin ta kai yaronta da wata yar uwarta wajen makwabta sannan ta garzata asibitin NAF."

Jami'ar Soja ta gamu da cizon maciji

Jami'ar Soja ta gamu da cizon macijiya cikin ban dakin gidanta dake barikin Soji, ta mutu Hoto: Punch Source: Facebook

Me ya faru da taje asibiti?

Majiya ta cigaba da cewa jami'ar ta mutu a asibitin ne saboda dalilai da dama wanda ya hada da rashin duba ta da wuri.

A cewar majiyar:

"Da ta isa asibiti, sai da aka dau lokaci kafin yi mata allurar maciji. Bayan rashin magani, na samu labarin cewa wanda ke da hakkin bada magunguna ba ya nan."

"Hakazalika sashen jikin da macijin ya cijeta na cikin dalilan da yasa ta mutu."

Yunkurin ji daga bakin Kakakin hukumar NAF, Edward Gabkwet, ya ci tura.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN