Type Here to Get Search Results !

Da duminsa: Lantarki ya kashe wani matashi da ya hau cabe domin satar wayar wuta


Wani matashi ya mutu nan take lokacin da ya hau caben wutan lantarki ya yi kokarin satar wayar wuta a garin Kobape da ke karamar hukumar Obafemi/Owode a jihar Ogun. Shafin isyaku.com.ya samo.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Lahadi 21 ga watan Nuwamba bayan jama'a sun wayi gari suka gan gawar tana lilo daga caben wutan lantarki.

Rahotanni sun ce babu wanda ya san mamacin kawo yanzu.

Sai dai Kakakin hukumar yansandan jihar Ogun Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai. Ya ce an sami gawar da wayar lantarki da ya fara yankewa.

Ya yi zargin cewa mamacin ya mutu ne garin yunkurin satar wayar lantarki.

Ya ce yansanda na ci gaba da bincike kan lmaarin bayan sun dauke gawar daga wajen da lamarin ya faru. 

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies