Da duminsa: An kashe Dogo Giɗe, ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga da suka sace yan makarantar Birnin Yauri jihar Kebbi kuma ya daɗe yana adabar jihohin arewa


Rahoton da muka samu daga PRNigeria ya ce an kashe hatsabibin shugaban 'yan bindiga Dogo Gide. An kashe shi ne a dajin Kuyanbana da ke jihar Kaduna. 

A watan Maris na shekarar 2018, Gide ya kashe hatsabibin shugaban yan bindiga a wannan lokacin, Buharin Daji, bayan hakan ne ya zama shugaban yan bindigan yankin. 

Wata majiya ta shaidawa PRNigeria cewa Gide ya mutu ne a ranar Lahadi bayan mataimakin kungiyarsa na yan bndiga, wani Sani Dan Makama ya bindige shi kamar yadda ya yi wa Buharin Daji. 

Tsohon shugaban 'yan bindigan ya dade yana adabar garuruw a jihohin Zamfara, Niger, Kaduna, Katsina da Kebbi tsawon shekaru. Majiyar ta ce: "Mataimakin Dogo Gide wanda ake kira Sani Dan Makama ne ya kashe shi bayan wani sabani da ya shiga tsakaninsu a dajin Kuyambana da ya hada Zamfara - Birnin Gwari da Dogon Dawa." Dogo Giɗe, hatsabibi shugaban ƴan bindiga ya haramta shan giya da kayan maye a wasu ƙauyukan Zamfara 

A baya, kun ji cewa Dogo Gide, hatsabibin dan bindiga, ya saka dokar hana siye da siyar da giya da sauran muggan kwayoyi a wasu garuruwan masarautan Dansadau da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara. 

Shugaban 'yan bindigan da ke zaune a dajin Kuyambana, da ya ratsa ta jihohin Zamfara, Kaduna, Niger da Kebbi ya kwace iko a garin Babbar Doka, Daily Trust ta ruwaito. Ya gargadi mazauna kauyukan cewa a bainar jama'a za a kashe duk wanda aka kama yana sayar da miyagun kwayoyi ko kuma shan su. 

Saurari karin bayani ... 

Source: Legit

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN