Da duminsa: An kashe Almajiri aka cire kwakwalwarsa, duba wadanda suka yi wannan aiki (Hotuna)


Wasu mutane da ake zargin matsafa ne sun kashe wani Almajiri dan shekara 11 mai suna Muhd Yunusa suka cire kwakwalwarsa a jihar Bauch. Shafin isyaku.com ya samo.

Lamarin ya faru ne a unguwar Dutsen Kofar Wambai da ke tsakar Birnin Bauch ranar Asabar 20 ga watan Nuwamba.

Jaridar Tribune ta labarta cewa wasu mutane guda biyu ne suka kira wasu Almajirai su biyu cewa su biyo su za su basu wani abu. Bayan sun isa wani waje mai duhu, sai suka kwade daya Almajirin da wani abu a kai sai ya fadi. Shi kuma daya Almajirin ya samu ya tsere daga wajen ya je ya gaya wa makwabta.

Bayan jama'a sun isa wajen sai suka tarar cewa mutanen sun kashe Almajirin kuma sun cire kwakwalwarsa suka gudu da ita suka bar gawarsa a wejen.

Nan take makwabta suka sanar da Yan sanda. Kakakin hukumar yansandan jihar Bauch SP Muhammad Ahmad Wakil ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce yansanda na gudanar da bincike. 

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN