Da duminsa: Daliban makarantar sakandare sun yi wa DPO ruwan duwatsu yayin fada tsakaninsu, sun fasa masa kai jina-jina


Dalibai yan makarantar sakandare a garin Abeokuta sun fasa wa (DPO) Alimeke Ignatius kai da duwatsu lokacin da ya je rabon fada tsakanin daliba yan makarantun sakanare guda biyu a jihar Ogun.

Shafin isyaku.com ya samo cewa yan makarantun sakandare na Egba Comprehensive High School da na Asero High School a birnin Abeokuta sun kaure da fada a tsakaninsu ranar Litinin 22 ga watan Nuwamb.

Rahotanni sun bayyana cewa daliban sun yi ta yi wa junansu ruwan duwatsu da sauran ababe, sakamakon haka suka haddasa cinkoson ababen hawa sakamakon datse hanya da lamarin ya haifar a Unguwar.

DPO Alimeke, na ofishin yansanda na Obantoko, ya jagoranci jamiansa domin su kwantar da rikicin daliban, sai dai su kansu sun sha ruwan duwatsu a wajen daliban lokacin da suka isa wajen da daliban ke fada.

Sakamakon haka aka fasa wa DPO kai aka kuma raunata wasu jami'an yan sanda. An garzaya zuwa asibiti da DPO tare da jami'an da suka sami raunuka domin samun kulawan ma'aikatan Asibiti.

Kakakin hukumar yansandan jihar Ogun Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamatin. Ya ce yan sanda ba za su kulle kowane dalibi ba saboda yara ne. Ya ce sai dai an tsare wasu domin a ja kunnensu tare da basu shawarwari.

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN