Type Here to Get Search Results !

Da duminsa: Adadin yawan wadanda aka kashe a Illela ya haura zuwa 43 sakamakon harin Yan bindiga (Hotuna)


Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya tabbatar da mutuwar mutum 43 sakamakon harin Yan bindiga a karamar hukumar Illela ranar Litinin.

Shafin isyaku.com ya labarta cewa ranar Laraba 17 ga watan Nuwamba, Tambuwal ya jagoranci tawagar manyan jami'an tsaro da na gwamnatin jihar Sokoto suka kai ziyarar ta'aziyya ga al'umman garin Illela da kauyukan da lamarin ya shafa.

Idan baku manta ba, mun kawo maku Labarin yadda Yan bindiga suka farmaki garin Illela da wasu Æ™auyuka' da ke makwabtaka da garin kuma suka kashe mutane 15 ranar Litinin. 


Sai dai wata da sanarwa da ta fito daga mai magana da yawun Gwamna Tambuwal, Muhammad Bello, ranar Alhamis, ya ce lokacin da Gwamnan ya kai ziyara Illela, adadin wadanda suka mutu ya kai 43.

Yan bindigan sun raunata wani Dagaci a harin da suka kai garin Illela da kauyukan Kalmalo, Munwadata, Sarma, Runji da Masasa. 

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies