Jaridar Dailytrust ta rahoto cewa yanzu haka ana cigaba da jin karar harbe-harbe a gidan gyaran halin Jos, jihar Filato.
Rahotanni sun bayyana cewa karar harbe-harben ya fara tashi ne da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin ranar Lahadi.
A halin yanzun jami'an tsaro sun mamaye baki ɗaya ilahirin yankin, inada suke cigaba da kula da zirga-zirgan mutane a yankin.
Da muka tuntuɓi kakakin hukumar gyaran hali NCoS reshen jihar Filato, Jeff Longdiem, kan abinda ke faruwa, ya yi alkawarin zai neme mu daga baya.
Cikakken bayani na nan tafe...
Source: Legit.ng