Da Dumi-Dumi: 'Yar Sanata Goje ta ajiye aikin Kwamishina a Jihar Gombe


Kimanin awa 24 bayan an kai wa mahaifinta hari, Dr Hussaina Danjuma Goje ta ajiye aikinta a matsayin kwamishinan muhalli da albarkatun daji na jihar Gombe.

A cikin wani gajeren sakon bidiyo da ta fitar a ranar Asabar, Hussaina ta ce ta ajiye aikin ne kan wasu dalilai na kashin kanta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ta yi wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya godiya bisa damar da ya bata na yi wa jiharta aiki.

Ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yau Asabar 6 ga watan Nuwamban 2021, ina son sanar da al'umma da kafafen watsa labarai cewa ni, Dr Hussaina Goje na mika takardar murabus di na a matsayin Kwamishinan Muhalli da Albarkatun ga Mai Girma Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, na ajiye aiki daga yau."
"Ina son sanar da cewa na ajiye aikin ne kan dalilai na kashin kai na. Da haka, ina mika godiya ta ga Gwamna Yahaya da ya bani damar yin aiki a gwamnatinsa."

A dai ranar Juma'a ne wasu da ake zargin yan daba ne suka kai wa mahaifinta, Sanata Muhamamd Goje hari bayan tare tawagarsa a hanyarsu na zuwa Gombe.

Amma rahotanni sun ce babu abin da ya same shi.

Rahotanni baya-bayan nan suna nuni da cewa, dangantakar da ke tsakanin Sanata Goje da gwamna Yahaya ta yi tsami a ‘yan kwankin nan.

'Yan daba sun hana Sanata Goje shiga garin Gombe, sun tare hanya suna ƙone-ƙone

Tunda farko, kun ji cewa wasu da ake zargin yan daba ne, a ranar Juma'a, sun hana Sanata Muhammad Goje shiga garin Gombe.

Goje, wanda ya tafi Gombe domin halartar daurin aure, ya dira a filin saukan jirage na Gombe a Lawanti misalin ƙarfe 10.40 na safe.

Daily Trust ta ruwaito cewa wadanda ake zargi yan daban ne sun tare babban titin Gombe-Bauchi kusa da International Conference Centre, sun cinna wuta a titi sun hana shiga ko fita daga Gombe.

Source: Legit.ng

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN