Boko Haram sun fara karbar haraji da sunan zakkah a hannun al’umma a Borno


Mazauna da manoman garin Damboa a jihar Borno sun soma biyan haraji da sunan zakkah ga ‘yan ta’addan Islamic State of West Africa Province.

Jaridar Daily Trust ta samu labari cewa kungiyar Islamic State of West Africa Province ta na karbar wadannan kudi ga mutanen da ke karkashin inda take iko.

A addinin musulunci, masu dukiya suna cire wani kaso daga cikin arzikinsu na kudi da amfanin gona duk shekara, su ba mabukata domin rage talauci a al’umma.

Wani babban jami’in gwamnati ya shaidawa Daily Trust cewa a halin yanzu, manoma da-dama suna karkashin ‘yan ta’addan kungiyar ISWAP a garin na Damboa.

Mutane ba su son gwamnati ta sani

“’yan ta’addan suna kyale mazauna yankin su yi noma, sai su karbi abin da suka kira haraji (kudin da ake ba mabukata duk shekara).”

“Suna karbar wannan daga hannun kowane manomi bayan ya samu amfanin gona.” - Jami’in.

‘Yan ta’addan Boko Haram a jihar Borno

Majiyar tace babu wani manomi da ya isa ya kauracewa wannan tsari da ‘yan ta’addan suka shigo da shi. Dole kowa ya bada wani kaso daga abin da ya noma.

Wani manomi mai suna Musa Mrusha da ya zanta da ’yan jarida, ya bayyana cewa mutanen da aka tursasawa biyan wannan zakkah, ba su so hukuma ta san batun.

“A lokutan baya, mayakan Boko Haram sun kashe mutane rututu a lokacin girbin gona. Shin a wannan shekarar ka ji irin wannan labarin?” - Musa Mrusha.

A farkon bara, ‘Yan IPOB suka zo gonar Mrusha, suka ce masa idan ya cire amfanin gona zai bada wani abu, ya kuma amince da wannan tsari hankalinsa a kwance.

Akasin yadda aka san mayakan Shekau da kashe mutane, 'yan ISWAP suna sa kayan sojoji, su karbi harajin hanya daga hannun direbobi da ke bin titunan Damboa.

Legit Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Domin samun labaran mu ta Whatsapp kai tsaye Latsa Link a kasa

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin Tuntubar mu ko aiko Labari LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu LATSA NAN

Shafin mu na Facebook facebook.com/isyakulabari 

Shafin mu na Twitter twitter.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN