Duba birnin da Musulmai suke jagoranci a Amurka


Yin tattaki a babban titin Hamtramck, da ke Michigan, tamkar yawon bude ido ne a duniya.

Kantin sayar da naman sausage na wani dan kasar Poland, da wurin da ake gasa kayan kwalam-da-makulashe na gabashin Turai na kusa da wani kantin mutanen Yemen, a kusa da shi kuma na wasu ƴan Bangaladesh ne da ke sayar da tufafi.

Ana iya jin kiran sallah daga masallacin da ke titin yayin da kararrawar wata coci da ke kusa ke kaɗawa.

"Wannan shi ake kira duniya a ƙaramin wuri" - kamar yadda aka sani yankin Hamtramck, cike yake da mutane daga sassa daban-daban, sannan akwai masu magana da harsuna sama da 30 a yankin.

A wannan watan, birnin mai cakuɗe da mutanen yankin gabas ta tsakiya da turai mai yawan jama'a 28,000 ya kafa tarihi - an zabi kansila da magajin gari musulmai, hakan ya sanya birnin ya zamo na farko a Amurka da wani musulmi zai jagoranta.

A baya ana nunawa musulmai tsangwama da kyara, sannu a hankali birnin ke cika da mutane har ya kasance kusan rabin al'ummarsa musulmai ne.

Duk da ƙalubalen tattalin arziki, da muhawara kan al'adu da mazauna daga addinai daban-daban, a Hamtramck haka ya sanya ya zama yankin da ake nazari a matsayin inda za a samu karuwar mutane daga dukkan ɓangarori a nan gaba.

Anya za a iya keɓe Hamtramck daga dokokin kasa?

Tarihi ya nuna Jamusawa ne suka fara zama a garin Hamtramck, kuma ya zamo yanki na farko da yawancin musulman Amurka.

Da zarar ka fara yawo a titunan birnin, babu abin da za ka gani a kofar kantina sai alluna ɗauke da rubutun Larabci da Bengali, a tagogin shagunan ɗinkakkun rigunan da akai musu ado irin na mutanen Bangladesh da dogayen rigunan larabawan Yemen na jallabiya, da sauran kayan ƙyalƙyali.

"Abu ne mai wuya ka ga mata sanye da dangalallen siket ko da zane a jikinsu, mata za ka gansu sanye da doguwar riga da nikabi suna tafiya a gefen titi.

Wannan ita ce rayuwarmu," in ji Zlatan Sadikovic, wani ɗan ci-rani daga Bosnia da ke aiki a kantin sayar da gahawa da ke Hamtramck.

Kashi-kashi

Wani gungumen dutse da aka ajiye a Detroit, wanda a fakaice yake birnin Hamtramck a baya ya kasance nan ne tsakiyar masana'antun kera motoci a Amurka.

A shekarun 1980 ne Cadillac Eldorado mutum na farko ya fara ginin majalisa a wajen.

A ƙarni na 20, yankin ya zama ɗan ƙaramin birnin Warsaw saboda yawan 'yan ci-ranin Poland da suka yi ƙaura daga can suke zaune domin gudanar da ayyuka daban-daban.

Har wa yau, birnin shi ne inda Fafaroma John Paul na biyu ya yada zango a lokacin ziyarar da ya kai a shekarar 1987. Tun daga shekarar 1970 har zuwa 1990 birnin cike yake da mutanen Poland.

A hankali, bayan shekara goma lokacin da kasuwar ƙera motocin Amurka ta fara janyewa, aka fara samun matasan attajirai Amurkawa ƴan asalin Poland suka fara sauya aƙalar kasuwancin daga wannan yankin.

Wannan sauyi ya janyo Hamtramck, ya zama yankin matalauta na birnin Michigan, amma sauƙin rayuwa a yankin ta ja hankalin 'yan ci-rani.

Shekaru 30 bayan nan, gagarumin sauyi ya samu Hamtramck, ya zamo yankin da Larabawa da mutanen yankin Asiya ƴan ci-rani suka mamaye, musamman daga ƙasashen Yemen da Bangladesh.

Har wa yau yawancin mazauna yankin kashi 42 ba a nan aka haife su ba zuwa suka yi, sannan an yi amanna da cewa sama da rabin mutanen mabiya addinin musulunci ne.

Zaɓar sabuwar gwamnati a garin Hamtramck alamu ne na gagarumin sauyin da ake samu sannu a hankali.

Kansilolin yankin sun hada da Amurkawa ƴan Bangladesh biyu da ƴan Yemen uku sai Ba'amurke ɗan Poland da ya karbi addinin musulunci.

Amer Ghalib da ya yi nasarar lashe kashi 68 na kuri'un da aka kada ya zama Ba'amurke ɗan Yemen da ya zama musulmin farko mai muƙamin magajin gari.

"Na yi farin ciki da wannan karramawa, abin alfahari ne a gare ni, zan kuma yi aiki yadda ya dace," in ji Mista Ghalib, mai shekaru 41.

Haifaffen wani ƙauye a Yemen ne, sun yi hijira a lokacin yana da shekaru 17, ya fara aiki a kamfanin sai da kayan motoci da ke kusa da Hamtramck.

Daga bisani ya koyi harshen Ingilishi, aka kuma ba shi horo a matsayin jami'in lafiya, a yanzu yana aiki a matsayin cikaken jami'in lafiya da ya san makamar aiki.

Hamtramck ya kasance yanki mai cike da mutane daga sassa daban-daban da addinai daban-daban da kuma al'adu da kowanne yake burin ganin ya yi riko da su.

Amanda Jaczkowski da ke cikin waɗanda aka zaɓa a yankin ta jaddada yadda mutane ke son al'adunsu.

"Har yanzu mutane na alfahari da al'adunsu, kowa da ka gani a nan yana riƙo da al'adarsa ba kuma tare da ya shiga haƙƙin wani ba."

"Idan kuka yi zaman kusanci irin wannan, dole ku haƙura ku mutunta dabi'u da al'adu da addinan juna ," in ji Mis Jaczkowski, mai shekara 29.

Sai dai magajin gari mai barin gado Karen Majewski, wanda ya shafe shekaru 15 yana mulkin yankin, ya ce Hamtramck ba kamar sauran wuraren kawa ba ne. "Dan ƙaramin wuri ne, akan kuma samu tashin hankali nan da can."

An samu rabuwar kawuna da rashin fahimta shekarar 2004, saboda kiran sallah da ake yi da lasifika mai karfin amo. Wasu sun yi kiran a haramta yi kamar yadda da aka haramta sayar da barasa da mashayar da ke kusa da masallaci lamarin ya janyo koma bayan tattalin arziki.

Shekaru shida da suka wuce, a lokacin birnin ya zama na farko a Amurka da ƴan takara musulmai suka yi nasara da gagarumin rinjaye, ƴan jarida daga sassa daban-daban na duniya sun yi ta kwarara Hamtramck.

Yawanci ana bayar da rahoton rashin zaman lafiya a yankin da musulmi ke zaune, a nan ne wani ɗan jaridar gidan talbijin ya tambayi Miss Majewski ko tana jin tsoron zama magajiyar gari.

Akwai rade-radin yiyuwar a sanya dokokin shari'ar musulunci a yankin.

Ta nanata cewa Hamtramck, yanki ne mai cike da hada-hadar mutane da kuma faran-faran, sannan a koda yaushe kofa bude ta ke ga duk wanda ke son kawo ci gaba a yankin.

Ofishin kiɗaya na Amurka, bai tattara bayanai game da addinai ba, sai dai tsirarun binciken da ka yi na yankuna, sun yi amanna akwai aƙalla musulmai miliyan 3.85 a Amurka a shekarar 2020, hakan shi ne kashi 1 da ɗigo 1 na al'ummar ƙasar baki ɗaya.

Daga nan zuwa shekarar 2040, Musulmi za su kasance na biyu addinin da suke da yawa a kasar baya ga mabiya addinin Kirista.

Shekaru 20 da kai harin 11 ga watan Satumba, har yanzu ana nunawa musulmai musamman Larabawa kiyayya a Amurka.

Kusan rabin musulmai Amurkawa sun bayyana cewa sun fuskanci cin zarafi ko kuna kyama, musamman a shekarar 2016 lokacin da shugaba Donald Trump ya bayyana ƙarara zai sanya dokar haramcin shiga ƙasar daga ƙasashen musulmai, a wani ɓangare na yaƙin neman zabensa.

Kusan rabin Amurkawa, sun ce ko dai ba su san wani musulmi ba, sai dai ƙalilan da suka san su da kuma yin mu'amala da su, sun san cewa addinin msulunci ba ya yaɗa tashin hankali.

Hamtramck Karamin misali ne na yadda ake nunawa addinin musuluncin ƙyama da ƙiyayya.

A lokacin da Shahab Ahmed, ya fito takarar muƙamin siyasa jim kadan bayan kai harin 11 ga watan Satumba, ya fuskanci ƙalubale ba kaɗan ba, an kuma yi ɗan ƙaramin yaƙi a lokacin.

"An yi ta rarraba takarda a ɗaukacin birnin, inda ake cewa ni ne ɗan ƙunar bakin wake na 20 da ban samu damar isa filin jirgin sama akan lokaci ba ,"inji Ba'amurken kuma ɗan Bangladesh.

Bayan faɗuwa zaben shekarar 2001, Mista Ahmed ya buga kofar gidan maƙwabcinsa, tare da gabatar da kan shi gare su. Shekaru biyu bayan nan aka zabe shi a matsayin musulmi na farko cikin madafun ikon birnin Hamtramck.

Tun daga lokacin, aka fara nuna goyon baya ga musulmai a birnin.

Ashekarar 2017, lokacin mulkin Donald Trump an haramtawa mazauna yankin yin zanga-zanga.

Sannu a hankali, ƙungiyar Musulmin Amurka ta samu gindin zama, aka kuma san ta a fagen siyasa.

A shekarar 2017, Minnesotan Democrat Keith Elliso ya zama namiji na farko a majalisar dokokin Amurka. A yanzu aƙalla akwai ƴan majalisa hudu a majalisar dokokin kuma dukkansu musulmai.

Tabar wiwi ta ƙara zama wani abu da ya janyo zazzafar muhawara a birnin. Kantina uku na al'ummar Musulmi da mabiya ɗarikar Katolika duk sun nuna rashin amincewa.

A daren ranar zabe, Amurkawa ƴan asalin Yemen sun kewaye Mista Ghalib, inda suka yi dandazon yin walima gabannin zabe, inda aka ci gasasshen nama da suran kayan kwalam. Kuma magoya baya da dama ne suka halarta sai dai dukkansu maza ne.

Mata ma sun taka muhimmiyar rawa a gangamin yakin neman zaben Mistra Ghalib, sai dai har yanzu akwai wannan batun kebewar maza da mata.

"Yaya birnin da mabiya addinin Musulunci suka fi rinjaye ke kallon mulkin Dimukradiyya? Kamar ko ina, akwai masu goyon baya akwai masu adawa, lamari ne mai cike da sarƙaƙiya," in ji Mista Jafri, wani mai shirya fina-finai.

Rahotun BBC Hausa

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN